Friday, September 2, 2016

(WACECE KHADIJAH LITTAFI NA DAYA NA NURA ISA S GARO)
1 Dakin asibitin ya yi shiru, ba ka jin motsin kowa sai kukan mace guda daya da ta sa mara lafiyan a gaba. yar dattijuwar matar dake gefen ta ita ma idanuwanta sun ciko da kwalla ta kalli likitan dake ta faman aikin gwaje, gwaje a kan mara lafiyan.
Ta ce,
Yanzu Doctor Ahmad kana nufin idan Nura yakai gobe be farka ba ze mutu?.
Doctor Ahmad ya danyi shiru kamar ba ya san Magana, sannan.
Ya ce,
Hakane hajiya, bana zatan in ya kuma awa ashirin da hudu be farka ba, ze kuma wani numfashi a duniya
Ya ba ta amsa a lokacin da ya ke kokarin gyara kwanciyar mara lafiyan.
Dattijiwar matar ta goge hawayan da ke ta fita da ga idanta sannan
Ta ce,
Bazan iya jure ganin Nura a cikin wannan hali ba Doctor, dan haka, ina san ka bincika min asibitin da zanje cikin fadin duniyar nan, kafin wadannan awanni su cika
Likitan ya kalleta ya ce,
Hajiya bana zatan duk asibitocin duniyar nan in zasu taru akan Nura akwai wani taimakwan da za su iya yi mai, domin kuwa abin dake faruwa a kanshi bakwan abune a duniyar ilimin likitanci ta duniya. a iya bincike na, lafiayarsa kalau ba abin dake damunshi, illa rashin kwarin jiki saboda tsawon lokacin daya dauka beci abinci ba,
Wasu tagwayan hawaye suka fito da ga idanuwanshi yai saurin sa gefen rigarsa ya goge, sannan ya ci gaba da cewa.
Dafarko na zaci barci ya ke, amman tsayin kwanakin da ya shafe be farka ba ne suka tabbatarmin ba lafiyarsa kalauba, nayi kokari na turawa babban sashin asibitin mu dake kasar England irin abinda na ke fuskanta akan mara lafiyan. bayan sun bincika suka tabbatar min da basu sami wata mafita ba game da wannan matsalar. Bayan haka suka sanar dani cewar tsayin kwanakin da ya dauka be ci komai ba in har ya kara awa ashirin da hudu be farka ba mutuwa ze yi, domin yanzu ha ka lakar jikinshi ta yi rauni sosai
Likitan ya na zuwa nan a zancensa dattijuwar ta fashe da kuka. yarinyar da ke gefen mara lafiyan kuma ta sa hannu ta na jijjiga mara lafiyan da karfi cikin kuka ta na ce wa.
Dan Allah Noor ka tashi, in ka mutu nima bazan iya rayuwa ba.
Da sauri Doctor Ahmad ya ture hannuwan yarinyar daga jikin mara lafiyan. sannan cikin fushi ya fara yi mata Magana.
Jijjigashin da ki ke ba ze sa ya mutu ba har sai kwanan shi ya kare. kar kiji an ce ba ze kara awa ashirin da hudu ba kiyi farin ciki. idan Allah ya yi akwai kwanan shi a gaba dole ya farka.
Yai shiru. wasu hawaye da yai kokarin 6oyesu suka samu damar sauka akan fuskar sa. muryarshi na rawa alamun kukan da ya ke ya fara cin karfinsa ya ci ga ba da ce wa.
Sau uku kina dukanshi ya na suma. kin ji mai manya-manyan raunuka sunfi a kirga. Amman bawan Allah nan be ta6a nuna miki damuwarsaba illa ma kokarin ganin ya kwantar miki da hankali da ya ke. Ke kuma hakan be sa kin janye aniyarki ta kokarin kashe shin da kike ba
Kuka ne yaci karfin Doctor Ahmad yai shiru ya fara kokarin saita numfashinsa da ke kokarin daukewa. Daya daga cikin nurses din da ke dakince ta ce,
Kayi hakuri ha ka Doctor ka san kana da ciwan zuciya, in ka sawa kanka damuwa ako da yau she jininka ze iya hawa.
Ba tare da ya kalle ta ba ya ce,
Ba komai Maryam nagode da kulawar da kike ba ni
Sannan ya waiga gun dattijuwar da har a lokacin bata daina kukan da take ba. ya na kokarin yi mata magana ne hannun mara lafiyan ya fara motsi. cikin sauri ya maida hankalinsa gun mara lafiyan domin kwana tara kenan da kawo mara lafiyan amman ko yatsansa be ta6a motsawaba duk da kokarin da likitan yai tayi na ganin ya farkar da shi, amman ya kasa cin nasara saboda yanayin da mara lafiyan ya nuna kamar ya mutu alhalin kuma ya na numfashi, illah rashin motsi da ga6o6insa ke yi, sai yanzu da idanunsa suka gane mai motsin da maralafiyan ya yi.

4 comments:

  1. (WACECE KHADIJAH LITTAFI NA BIYU NA NURA ISA S GARO) 45 daman ta san halinshi da san yawo. abu daya ne ya tayar mata da hankali kar a kirata bayanan dan ba ta san yadda za ai a kar6i kyautar ba kuma.
    Nan da nan ta fara kalle, kalle a cikin jamaa ko zata hango shi. idanuwanta ne suka tsaya akan wata karamar yarinya.
    Fara ce kamar balarabiya, ba zata wuce shekara shida ba. sanye take cikin wata doguwar riga wacce take jan kasa saboda tsayinta, sannan kanta anyi mata parkin din dogon gashin kanta sannan an sa mata wani dan karamin hijabi. suna hada ido Khadijah taga yarinyar ta tsaya ta kura mata ido tana mata murmushi.
    Nan take Khadijah ta ji kaunar yarinyar ta shiga ranta. itama ta daga mata hannu tana murmushi sannan ta kira yarinyar.
    Da gudu yarinyar ta taho tana zuwa ta buda hannayanta, Khadijah ta dauketa.
    Assalamu alaiki ya Ummi. yarinyar ta ce sannan ta kama kan Khadijah da hannayenta guda biyu, ta kara bakinta a kumatun Khadijah ta yi mata kiss.
    Wash!. Khadijah ta ce, domin kafin ta dauki yarinyar ta lura da dam6areran jambakin da akai wa yarinyar kwalliya da shi.
    Jin Khadijah ta ce wash ne ya sa yarinyar ta kalleta fuskarta tana nuna damuwa ta ce,
    What is wrong mom?.
    Khadijah ta yi murmushi ta ce,
    Ashe ni yau yar turawa na dauka.
    Yarinyar ta kyalkyale da dariya ta ce,
    Babana ya ce, i am linguist. ina jin yare da yawa. kinga ina jin Hausa, Arabic, English, Spanish, French. kinga harma da fillanci duk ina ji ya koya min, in ze kirani sai ya ce min ware mi dille.
    Khadijah ta yi dariya, jin bayanin da yarinyar take mata a zuciyarta ta ce,
    yau na hadu da wacce tafi Abulkhair surutu.
    Ta fara wasa da dogwan gashin kan yarinyar da ya kwanta har gadan bayanta. sannan ta ce,
    to ya sunanki?.
    Ummulkhair. yarinyar ta bata amsa.
    Khadijah ta ce,
    nice name, amman ya sunanki na gaskiya? dan mafi akasari Ummulkhair ana amfani da shi ne wajen yin wakilcin suna.
    yarinyar ta toshe bakinta da hannu biyu. ta ce,
    Tafdijam! rufamin asiri Babana ya ce min karna fadawa kowa sunana.
    Khadijah tayi dariya saboda mamakin surutun yarinyar ta ce,
    Waye Baban naki?.
    yarinyar ta ce,
    Baba.
    Khadijah ta ce,
    Ya salam ai Baban kowa ma sunanshi Baba amman agunshi, ni sunan Baban na ki za ki fada min
    Yarinyar ta ce,
    Babana ya hanani fadin sunanshi shima. kin gafa sai da na yi ta yi mai kuka na ce ya kaini gun Mama ta. shine ya kawoni ya nuna min ke ya ce min kece Mamata.
    Mamaki ne ya kama Khadijah ta ce mata,
    to ina Baban na ki ya ke?.
    yarinyar tasa hannu ta nuna mata inda ta baro. Khadijah ta kalli wajen taga duk maza ne amman bata gane wanda yarinyar take nufi ba, sai ta ce,
    Waye daga cikin su?.
    ya salam Dad is noware found, may be he left for some purpose. ba Babana acan kila yaje wani wajen

    ReplyDelete
  2. hmmm littafi yayi dadi sosai Allah ya kara basita

    ReplyDelete