ZAHIRIN KAUNA
ZAHIRIN KAUNA
Nura Isah S. Garo
1(ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA DAYA, NA NURA S GARO)Kallo daya zaka yi wa fuskarta kasan akwai matsananciyar damuwa a tare da ita. Barrister Fatima Zahra Muhamma kenan, daya daga cikin gogaggu kuma kwararrun Lauyoyin da ake ji da su a nan gida Nigeria da ma sauran kasashen da ke makwabtaka damu sannan kuma ‘ya guda daya ga marigayi tsohon shugaban ‘yan sandan kasarnan.
Fara ce mai matsakaicin tsayi, tana da dogwan hanci da ‘yar faffadar fuska tare da yalwar gashin kai wanda ta yi parkingdinshi ta kwantar da shi zuwa gadon bayanta.
Tayi wata bayyananniyar ajiyar zuciya lokacin da ta karasa gaban tafkeken hotan Mahaifinta da kekafe a bangon da ke arewacin falon ta kura mishi ido tana kallonshi na dan wani lokaci. A zaune ya ke a cikin ofishinsa kasancewar lokacin da a ka dauki hotan yana tsaka da aikinsa a matsayinsa na shugaban ‘yan sandan kasar Nigeria.da murmushi bayyane a kan fuskarsa wanda hakan ke da nasaba da irin nasarorin da ya samu.
“ki kasance mai gaskiya da rikon amana Fatima, wadannan ne makaman da na rike har na kawo matsayin da nake na shugabancin rundunar ‘yansandan kasarnan, na tabbata in zaki yi riko da wadannan abubuwa biyu zaki samu nasarorin da baki ta6a tsammaniba a rayuwarki”
Barrister Zahra ta yi ajiyar zuciya lokacin da ta ke tuno irin nasihar da akoda yaushe Mahaifinta ya ke yawan yi mata a kan ta kasance mai gaskiya da rikon amana domin samun nasara a cikin rayuwarta, amman ya za ta yi da wannan sarkakkiyar shari’ar da ta tunkarota? Wannan ce tambayar da ta wuni tana yiwa kanta tun wayewar garin ranar lokacin da wani saurayi ya kirata a waya yake rokonta a kan ta taimakeshi ta ceto rayuwar Mahaifinsa wanda ke tsare a sashen masu manyan laifuka na ofishin ‘yan sanda ana tuhumarsa da laifin aikata kisan kai.
Ta kara yin wata sassanyar ajiyar zuciya a karo na biyusannan ta juya ta jingina bayanta a jikin bangon falon saitin inda hotan Mahaifinnata ya ke ta daga kanta sama tare da dulmiyawa cikin duniyar tunani.
Shekararta dai-dai har bakwai tana aikin shari’a amman bata ta6a gamuwa da sarkakkiyar shari’a irin wannan ba, bata ta6a haduwa da tashin hankali kwatan kwacin wannanba. Me ya ke shirn faruwa da ita ne?
2(ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA DAYA, NA NURA S GARO) Sallamar da ta ji anayi ce ta katse mata tunanin da ta ke, ta mayar da kallonta bakin kofar tare da amsa sallamar domin bawa wanda zai shigo izinin shigowa.
“amin wa’alaiki assalam, Barrister, bismillah shigo”
Barrister Zahra ta amsa sallamar tare da bayar da izinin shigowa ga mai yin sallamar lokacin da ta fuskanci kawarta, aminiyarta, kuma abokiyar aikinta Barrister Halimatussa’adiyya Mahmoud ce ta ke yin sallamar wacce a dabi’unta ba ta shiga daki ko falon mutum har sai ya bata izini domin yin koyi da biyayya ga umarnin fiyayyen halitta Manzon Allah Annabi Muhammad (S.A.W).
Barrister Halima ta shigo tana tafiya a hankula cikin nutsuwa tare da tauna cingum din da ke bakinta cikin gwaninta, fuskarta sanye da farin tabarau wanda aka kera jikinsa da narkakkiyar azurfa mai daukar ido.Ba sai ka tambaya ba kallo daya zaka yi mata kasan ta amsa sunanta na zama daya daga cikin manya manya kuma gogaggun lauyoyin kasar Nigeria.wata koriyar atamfa dinkin doguwar riga ce a jikinta wacce akai mata ratsin ado da wasu fararen duwatsu tun daga saman wuyan rigar har zuwa kasanta. fuskarta dauke da murmushi wanda baka rasata da shi a ko da yaushe kasancewarta mace mai yawan fara’a da barkwanci, ga iya tsara magana da fitar da lafazin bakinta yadda mai sauraronta zai gamsu da duk bayanan da ke fita daga bakinta.
Ganin alamun damuwar da ke bayyane a kan fuskar Barrister Zahra ne ya sa Barrister Halima ta sassauta murmushin kan fuskarta a yayin da ta kekarasawa gaban aminiyartata ta dafa kafadarta da alamun mamaki bayyane akan fuskarta ta ce,
“lafiya Zahra, Meke damunki na ga kin shiga cikin damuwa da firgici haka wanda tunda nake a rayuwata ban ta6a ganinki a cikin kwatan kwacin irinsa ba?”
Barrister Zahra ta yi ajiyar zuciya tare da nunawa Halima kujerun da ke jere reras sun yiwa falon kawanya ta ce,
“doguwar magana ce Barrister yakamata mu samu waje mu zauna domin halinnan da kika ganni a ciki wunin ranar yau haka na yi shi a karshe na yanke shawarar kiranki domin ance hannu biyu maganin kazamar miya, kuma abokin kuka shi ake fadawa mutuwa”
3(ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA DAYA, NA NURA S GARO)Da sauri Barrister Halima ta samu kujera ta zauna yayinda lokacidaya murmushin da ya rage a kan fuskarta ya yaye, matsananciyar damuwa ta samu gurbin zama a kan fuskarta domin ta san duk abunda da ya jefa kawarta cikin wannan hali na damuwa to ba karamun abu ba ne.
Barrister Zahra ta samu karamar kujerar da ke ajje a gefen wacce Barrister Halima ke zauneitama ta zauna suka fuskanci juna sannan ta fara yi mata bayani cikin nutsuwa tayadda kawartata za ta fuskanci abunda ta ke fada.
“wata sarkakkiyar shari’a ce ta tunkaromu Halima”
Barrister Zahra ta ce da kawartata lokacin da ta ga ta gama kaguwa domin jin abunda ta ke son sanar da ita.
“wacce irin shari’a ce wannan Zahra?”
Halima ta tambayeta cikin gaggawa da alamun mamaki karara a kan fuskarta.
“shari’ar kisa!”
Barrister Zahra ta bata amsa, ganin Halima ta yi shiru tana kallonta ne ya sa ta ci gaba da cewa,
“da misalin karfe goma na safiyar yau ne wani saurayi ya kirani yana kuka tamkar ransa zai fita yana rokona akan na taimaka na zamo lauyar da za ta kare Mahaifinshi”
Barrister Zahra ta tsayar da bayanin da ta ke yi ganin wani tattausan murmushi na bayyana a kan fuskar Barrister Halima wacce ta ci gaba da tauna cingum din da ke bakinta cikin salo da gwaninta irin ta gogaggu kuma wayayyun lauyoyin da suka san aikinsu.
“gaskiya kin ban mamaki Zahra, wannan dalilin ne ya sa hankalinki ya tashi duk ki ka rude kamar wata sabuwar lauya?”
Jin ta yi shiru bata amsa mata tambayar da ta yi mata ba ne ya sa Halima ta ci gaba da cewa,
“to in kin manta bari na tunatar da ke: ke ce dinnan dai Barrister Fatima Zahra Muhammad, ‘yadaya a wajen Marigayi I.G Muhammad Amin da matarsaJustice Aisha Sagir, kin shafe shekarudai-dai har bakwai kina aikin lauya, kin fuskanci shari’o’i masu hatsari da wuya, kin goga da manya manyan lauyoyin Senior Advocate of Nigeria da akafi sani da SANamman ba wanda ya ta6a nasara a kanki”
4(ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA DAYA, NA NURA S GARO) Barrister Halima ta yi shiru tare da dafa kafadar Zahra har a lokacin da murmushi ke karabayyane a kan fuskarta ta ci gaba da cewa,
“meye abun tsoratarwa a shari’ar kisa? Ba yau kika fara fuskantar irin wannan shari’ar ba kina yin nasara a kanta illah abu daya da na sani shi ne bakya kar6ar shari’ar mutum mara gaskiya. Meye bayani akan kisan da aka yi?”
Jikin Barrister Zahra a sanyaye alamun kirarin da Barrister Halima ta yi mata bai ratsata ba ta fara yi mata bayani kamar yadda saurayin ya sanar da ita.
“Umar Mukhtar sunanshi budurwar tashi kuma Suhailat Adnan sun fara soyayya wata biyar da suka gabatabai saniba ashe Mahaifin yarinyar abokin gabar Mahaifinsa ne, lokacin da aka fara shirye shiryen aurensu sai Mahaifin Suhailat ya gane ko shi dan waye ya ci mishi mutunci ya tozartashi a karshe ya sa Suhailat ta daina kulashi. Ganin irin damuwar daUmar ya shiga na rashin kulashi da Suhailatta ke ne yasa Mahaifinsa ya bi bayanta har cikin gidansu a gaban Mahaifinta da Mahaifiyarta ya sanar da ita cewar ko ta amince da aurendansa ko kuma shi ne ajalinta. kwanahudu da yin hakan Suhailat tana tafiya a cikin mota Mahaifin Umar yana biye da ita a baya ya daki motarta da karfi motar Suhailat ta fada cikin kwalbatin kwatar da ke gefen titi glass ya zubo mata a jiki, kanta ya daki sitiyarin motar inda bayan wasu mintuna da kaita asibiti rai ya yi halinsa. Kin ji yadda abun ya faru Barrister”
Halima ta girgiza kai babu alamun karayako fargaba a kan fuskarta ta fara lissafi da yatsunta tana nunawa Barrister Zahra.
“kinga mun samu intension da action a lokaci daya, amman wannan bai isheki hujjar da za tasa ki fita da ga cikin hayyacinkiba Barrister, karki manta da cewa komai yana iya kasancewa duk da Mahaifin Umar ya yi furuci kuma ya aikata hakan bai ishi hujjar da za ta sa a ce yana sane ya kashe Suhailat ba. Zamu iya amfani da kwarewa da gogewarmu mu gano gaskiya, daga karshe kiga munyi nasara. Amman abun tambayar yanzu ta ina zamu fara?”
“ban gane ba?”
Barrister Zahra ta ce mata da alamun rashin fuskantar abunda Barrister Halima ke nufi.
“ina nufin yana da kyau mu zauna da shi UmarMukhtardin domin ya yi mana cikakken bayani akan alakar Mahaifinsa da Alhaji Adnan”
5(ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA DAYA, NA NURA S GARO) Barrister Zahra ta girgiza mata kai yayin da damuwa ke kara bayyana a kan fuskarta ta kalli Halima ta ce,
“duk bayaninnan da na ke miki ban san waye Umar Mukhtar ba, ta waya mukai magana da shi, na yi saurin amince mishi ne ganin yanayin halin da ya ke ciki yana neman taimako domin kuka ya ke sosai kamar wani karamin yaro. Ya cemun karna damu da sanin ko shi wane ne zan sanshi amman sai nan gaba sannan ya kirani da lambar wayarkasar Romania a karshe ya kar6i lambar Accountdina ya turamun Naira Milliyan talatin. Abun mamakin shi ne kudin da ya yi mun transfer duk da foreignaccount ne kuma da na tambayeshi ya ce mun yana Nigeria amman ya bani hakuri akan bazan samu damar ganinshi ba”
Barrister Zahra ta yi ajiyar zuciya ganin yadda Halima ta kara nutsuwa tana sauraronta domin jin irin zunzurutun makudan kudin da Umar ya bayar domin a ceci rayuwar Mahaifinsa. Zahra ta ci gaba da cewa,
“bawai kudin da Umar ya bayar ba ne suka sa zan shiga wannan shari’ar ba, haka kawai nakeji a jikina cewar akwai kamshin gaskiya tattare da shi da Mahaifinsa duk da ya 6oye mun hakikanin ko shi wane ne”
Barrister Halima ta yi murmushi tare da tauna cingum din da ke bakinta cikin gwaninta ta ce,
“aitunda har ya bada wadannan makudan kudadan ya fanshi kansa ba sai mun san ko shi wane ne ba.yanzu aiki ya rage ya namu dole mu mike tsaye domin ku6utar da Mahaifinsa indai har muka tabbatar da gaskiyarsa. Amman abun tambaya a nan shi ne wane ne Barristan da zamu kara domin musan ta hanyar da zamu biyo mishi?”
“Barrister Haidar M Aliyu (SAN)…”
Zahra ta bata amsa cikin sarkakkiyar murya yayinda alamun damuwar da kekan fuskarta kekara munana.
“Master of law…”
Barrister Halima ta kirashi da lakabun da mafiya yawan alkalai, Barristers da lauyoyi ke kiransa da shi saboda kwarewa da iya aikinsa ta fuskar shari’a. lokaci daya murmushin da ke kan fuskarta ya yaye ta daina tauna cingum din da ke bakinta domin yadda ta ji hakoranta sunyi mata nauyi ga wani dandanon daci da ta ji cingum din ya fara yi mata a baki wanda ta yi saurin sa hannu ta cireshi ta ajje a kan karamun tabledin da ke ajje a gefensu, bata mayar da kallonta kan Zahra ba sai da ta tabbatar da ta cire faringlassdin da ke makale a kan fuskarta domin wani nauyi da ta ji ya fara ga dishi dishin da ta ke gani wanda ta alakanta dukkan hakan akan faringlassdin wanda aikinsa ya karawa mutum karfin gani.
No comments:
Post a Comment