Thursday, September 8, 2016

LITTAFIN ZAHIRIN KAUNA NA DAYA 16 to 20


ZAHIRIN KAUNA
Nura Isa S Garo

16(ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA DAYA, NA NURA S GARO) “shin ko mece ce hujjarka ta cewa [anka bai turomu wajenka domin muyi narasa a cikin wannan shari’a ba, duk da makudan kudin da ya bayar da irin kuka da tashin hankalin da ya shiga lokacin da ya ji labarin an kamaka ka aikata wannan laifi?” Alhaji Mukhtar ya yi murmushi wanda har sai da fararen hakoran da ke jere a cikin dasashin bakinsa suka bayyana. Ya ce, “tambayarki bata yi daidai da irin tambayoyin da ya kamata a ce kinamunba ‘yata, amman domin na cire muku dukkan wani shakku daga cikin zuciyarku yana da kyau na sanar muku” Ya danyi shiru yayinda murmushin kan fuskarsa ya dauke, ya mayar da hankalinsa gaba daya kan Barrister Halima sannan ya ci gaba da magana cikin nutsuwa, “Allah Ubangijin da ya halicci sammai da kassai shi ya fi sona fiye da kowa, sai manzonmu Annabi Muhammad (S.W.A), ina tabbatar miki na ukun shi ne Umar Mukhtar. Yana bala’in sona fiye da yadda bakina zai furta miki Barrister, zai iya bada rayuwarsa domin ya fanshi raina saboda irin kaunar da ya ke yi mun. na ba shi tarbiya irinta addinin musulunci don haka ba zai ta6a goyan bayana akan laifin kisan kaiba sai dai ya dauki wannan laifi nawa a matsayin wata jarrabawa daga cikin jarrabawon Ubangijinsa, rabani da shi ba karamar jarrabawa ba ce a gareshi domin ba shi da kowa sai ni” Barrister Zahra da Barrister Halima suka yi ajiyar zuciya a lokaci daya yayinda tausayin Umar ya kara dabaibaye zuciyarta ta kalli Alhaji Mukhtar ta ce, “Alhaji ko zaka iya yi mana bayani akan yadda wannan lamari ya kasance da kai tun daga lokacin da kai furucin zaka kashe ‘yar Alhaji Adnan wato Suhailat zuwa lokacin da ka daki motarta ta yi hatsari?” Alhaji Mukhtar ya kalli Barrister Zahra ya ce, “hakan ta faru ne lokacin da [ana ya kirani ya ke sanar da ni cewar Alhaji Adnan ya ce bazai ba shi auren ‘yarsaba. A lokacin da na yi amfani da wannan hadisin na manzon Allah (S.A.W) da sahabinsa yake cemishi ka bani shawara manzon Allah ya ke cemishi kar ka yi fushi har sau uku da duk haka bata faruba. Domin kuwa muna gama waya da Umar na kasa zaune na kasa tsaye har sai da zuciyata ta rayamun na je har gidan su Suhailat na yi mata barazana da zan kasheta ko za ta ji tsoran mutuwa ta amince da auren Umar. Hakan kuwa akai na fita daga gida ban zame ko ina ba sai gidan Alhaji Adnan inda na same su a falon gidansa shi da matarsa da ‘yarsa na fadi abunda ke cikin zuciyata. Duk sun tsorata da jin kalamaina inda na tafi na barsu cikin zulumi. Kwana hudu da faruwar hakan ina cikin tafiya a motata kawai sai ji na yi na daki mota wacce nan ta ke ta fada cikin kwalbatin magudanar ruwan da akayi domin wucewar ruwa. Hankalina a tashe na fito mutane suka taimakamun aka fito da su aka sa su a motata na kaisu asibiti. Hankalina ya yi bala’in tashi a lokacin duk na rude ban gane wace ce ba duk da daman ba wani saninta na yi ba domin ganin farko da na yi mata shi ne lokacin da na je har gidansu na ce zan kasheta. ban tashi gane cewar Suhailat Adnan ba ce sai da Mahaifinta da Mahaifiyarta suka shigo cikin asibitin hankalinsu a tashe Mahaifiyar yarinyar tana kuka” 17(ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA DAYA, NA NURA S GARO) Alhaji Mukhtar Maidugu ya yi shiru tare da yin wata bayyananniyar ajiyar zuciya sannan ya ci gaba da cewa, “na shiga halin rudu da danasanin furucina a lokacin da ba shi da amfani, nasan bawanda zai yarda cewar ba da sanina na daki motar Suhailat ba, har [ana Umar baya goyan bayana domin yana kafa hujja da cewar duk abunda na ce zanyi sai na yi shi ko mene ne. ni kaina ba zan iya gaskata kaina ba Barrister” Barrister Zahra da Halima suka yi shiru sun nutsu suna sauraronsa har ya kai karshen bayanin da ya ke musu sannan Barrister Zahra ta ce, “mun gode da hadin kan da ka bamu, gobe insha Allah zamu hadu a kotu” “Allah ya kaimu” Alhaji Mukhtar ya ce tare da yi musu sallama sannan ya juya ya koma inda ya taso ya zauna ya ci gaba da lazimi da ambaton Allah kamar yadda suka zo suka tarar da shi. Barrister Halima ta kama hannun Barrister Zahra suka juya suka fita daga cikin jerin dakunan kurkukun. “yanzu kuma sai ina kenan?” Barrister Halima ce ta tambayi Barrister Zahra lokacin da suke kokarin fita daga cikin wajen. “sashen tattara bayanai zamu shiga domin duba irin bayanan da ‘yan sanda suka yi a kan yadda hatsarin ya faru” Barrister Zahra ta bata amsa a lokacin da suka tsaya a kofar shiga ofishin da ta ke fada. “hakan ya yi kyau” Barrister Halima ta ce sannan ta sa hannu ta bude kofar suka tura kai suka shiga sashen ‘yan sandan da ke sashen suka dunga gaishe da su suna amsawa cikin sakin fuska. Kai tsaye 6angaren babban jami’in da ke kula da shiyyar suka zarce wanda suka sameshi ya dukufa sai aikin rubuce rubuce ya ke kamar yadda ya saba, bayan sun yi mishi sallama ne ya amsa cikin sakin fuska yana murmushi ya mike tsaye domin girmamawa ga manyan lauyoyin guda biyu sannan ya basu waje suka zauna. “muna son bayanan da kuka dauka akan hatsarin da ya afku tsakanin Alhaji Mukhtar Mai Gaskiya da Suhailat Adnan” Barrister Zahra ta yi saurin yi mishi magana lokacin da suka zauna domin gajarce lokutan da suke 6atawa a duk sashen da suka shiga. Jami’in ya yi saurin jan Computer da ke gabansa ya fara daddannawa bayan wani dan lokaci ya binciko bayanan da ke ajje a cikin computar ya buga a takardu ya mika musu sannan ya dauko hotunan motar da akai hatsarin tare da hotunan Suhailat da aka dauketa tun daga asibitin har zuwa gida da inda aka sata a kabari ya mika musu suka kar6a suna duddubawa cikin nutsuwa. Bayan sun gama duddubawa ne Barrister Halima ta kalli Jami’in mai suna ASP Ibrahim ta ce, 18(ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA DAYA, NA NURA S GARO) “Ibrahim zamu tafi da wadannan hotunan domin kara nazari da bincike a kansu” “bakomai Hajiya daman mallakarsu yana da amfani” ASP Ibrahim ya bata amsa sannan ta bude cikin jakar da ke ajje a kan cinyarta ta saka hotan ta daga kanta ta kalli Jami’in dan sandan ta ci gaba da cewa, “a hannun wa case dinnan kuwa ya ke Ibrahim?” “ASP Mubarak Ameen” Ibrahim ya bata amsar tambayar da ta yi mishi tare da kara nutsuwa domin ya san a ko da yaushe za ta iya yi mishi wata domin yasan halinsu ne na lauyoyi. Barrister Halima ta gyada kai cikin gamsuwa da amsar da ASP Ibrahim ya bata sannan ta ce, “wanne likita ne ya aunata ya tabbatar da cewar ta mutu?” “Doctor Kabeer Abdullahi” “Ya salam…” Barrister Zahra ta ce cikin sauri tare da dafe kanta da hannayenta bibbiyu saboda sara matan da ta ji ya yi lokaci tsaya. “lafiya Barrister?” ASP Ibrahim ya tambayeta a hanzarce tare da mayar da hankalinsa kanta. “bakomi Ibrahim kaina na ji ya fara sarawa bana jin dadi sosai” Barrister Zahra ta ba shi amsa tana dan yatsina fuska don kar jami’in dan sandan ya fahimci halin rudanin da ta shiga tun gabannin jin sunan ASP Mubarak da Doctor Kabeer a cikin case din. Barriser Halima da tuni ta gama fahimtar halin da aminiyartata ta shiga ta kalleta a hankalce ta ce, “ko dai sai kin kara shan magananin nan ne Barrister?” “ina kyautata zaton haka sai dai kuma na mantoshi a mota in mun fita na sha” Barrister Zahra ta bata amsa. “Allah ya sauwake, ya baki lafiya” ASP Ibrahim ya ce fuskarsa na nuna alamun tausayi. “ameen” Suka amsa gaba dayansu sannan Barrister Halima ta kalleshi ta ce, 19(ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA DAYA, NA NURA S GARO) “to mungode ASP zamu tafi sai mun kara waiwayarka kenan idan bukatar hakan ta taso” “shikenan Hajiya nagode Allah ya saka da alkairi” ASP Ibrahim ya ce mata a lokacin da suka mike, Barrister Halima ta rataya jakarta a kafada sannan ta kama hannun Barrister Zahra wacce ta kasa yin magana, suka juya suka fita ASP Ibrahim ya bisu da kallo har sai da suka fita daga cikin sashen tattara bayanan sannan ya yi ajiyar zuciya ya dukufar da kai ya ci gaba da yin aikinsa. Fitarsu daga cikin sashen bincikar masu manyan laifuffukan na bompai ke da wuya suka shiga motarsu, Barrister Halima ta kar6i tukin kasancewar ta fahimci hankalin kawartata ya yi matukar tashi wanda a matsayinsu na masana doka tasan doka bata yarda mutum ya yi tukin mota a cikin irin wannan halin ba. Sai da Barrister Halima ta saita kan sitiyarin motar a kan titin Hadejia Road daura da Wellcare Kano sannan ta juya ta kalli Barrister Zahra a nutse ta fara yi mata magana cikin nutsuwa. “na fahimci kin tayar da hankalinki da yawa Barrister, kar ki manta shari’a sa6anin hankali ce ba duk abun da mutum ke zargi ba ne ya ke kasance gaskiya” Barrister Zahra ta yi wata bayyananniyar ajiyar zuciya ta kalli Barrister Halima ta ce, “abun ne ya ke bani tsoro Halima, a ce duk wanda case dinnan ke hannunsa mutumin kirki ne, jajirtacce ne, sannan mai kokarin ganin ya tabbatar da gaskiya ne. Kai hatta Alhaji Mukhtar da ya aikata kisan shima mai gaskiya ne idan ki kai la’akari da yanayi da furucin bakinsa zaki san ba da gangan ya aikata wannan laifiba” Ta fara yi mata lissafi tana nuna mata da hannu. “da farko kinga lauyar da zamu yi shari’ar da shi Barrister Haidar Aliyu, kowa ya san wane ne shi a zahirance, ga alkalin da zai yanke hukuncin shari’ar Justice Musaddiq, dan sandan da ya yi bincike a kan case din ASP Mubarak, likitan da ya dubata ya tabbatar ta mutu Doctor Kabeer” 20(ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA DAYA, NA NURA S GARO) Barrister Zahra ta yi shiru tana girgiza kai fuskarta bayyane da alamun damuwa ta ci gaba da cewa, “zan iya rantse miki duk cikin wadannan mutanen da na lissafo bawanda zai iya kar6ar koda naira biyar ne domin ya 6oye gaskiya, sannan kowa kwararre ne wajen aikinsa ballantana na ce an samu kuskure a cikin ayyukansu” Barrister Halima ta gyada kai domin gaskata abunda kawartata ta ke fadamata sannan ta ce, “na lura da haka wallahi tun ina jin tsoro harma na daina jin tsoro domin ke da kanki da ki ke kare hakkin wanda ya aikata laifin kema mai gaskiyace abun dai da na yarda da shi shi ne gaskiya da gaskiya ce za ta kara a wannan lokacin sai dai muyi fatan Allah ya nuna mana gaskiya ya bamu ikon binta” “ameen” Barrister Zahra ta amsa mata a lokacin da Barrister Halima ta tsaya a bakin kofar gidansu Zahra ta danna hon domin mai gadi ya bude musu gate su shiga. Da sauri kuwa ya bude yana mai gaggawa Halima ta kalleshi a kokarinta na shiga gidan ta ce mishi, “dan tsaya karka kulle mai gadi yanzu zan fita” “to Hajiya” Mai gadin ya amsa mata cikin girmamawa. Barrister Zahra ta kalleta ta ce, “bazaki bari mu shiga cikin gida mu ci abinci ba sai ki tafi?” Barrister Halima ta girgiza mata kai hade da cewa, “gaskiya lokaci ya kure Barrister ya kamata na je gida na yi abunda ya kamata kinga dai bamu da lokaci gashi gobe karfe goma na safe za mu shiga kotu” “haka ne” Barrister Zahra ta ce, a lokacin ne Barrister Halima ta samu waje ta yi parking din motar, ta cire mukullin ta mika wa Zahra sannan ta sa hannu a cikin jakarta ta dauko hotunan da suka kar6o a wajen ASP Ibrahim ta mika mata. “ga wadannan hotunan ko zaki yi wani amfanin da su” Barrister Zahra ta sa hannu ta kar6i hotunan da Halima ke miko mata sannan ta ce,

No comments:

Post a Comment