Saturday, September 10, 2016

ZAHIRIN KAUNA LITTAFIN NURA S GARO


UNIVERSITY OF INFORMATION TECHNOLOGY KANO

BARKA DA ZUWA SHAFIN LITATTAFAN MARUBUCI NURA ISA S GARO

LITTAFIN ZAHIRIN KAUNA 21 (ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA BIYU, NA NURA ISA S GARO)uwana ya umarceni, Mahaifiyata ta ja hannuna muka doshi wajen da motarta take, Umar da Mahaifinmu suma suka juya zasu inda motar Mahaifinmu take, har sun bude motar zasu shiga Mahaifiyarmu ta canza shawara don haka ta juya ta kalli Mahaifinmu dake kokarin saka Umar a gaban mota ta kira sunanshi cikin sassanyar muryarta. “Alhaji!” Da sauri Mahaifinmu ya juyo ya kalleta da murmushinsa da ba’a rabashi da shi a ko da yaushe ya ce, “na’am Hajiya” Mahaifiyarmu ta kama hannuna muka karasa wajen da Mahaifina da Umar ke tsaye ta mika mishi ni sannan ta sa hannu ta kar6i Umar daga hannunsa ta ce mishi. “yau canji za a yi ka dau Umar ni na dauki Aliyu” Mahaifinmu ya fadada murmushin kan fuskarsa yana kallonta cikin nuna kulawa ya ce, “shikenan Hajiya ammanfa ki rikemun Babana da kyau ki kulamun da shi, kar ki bar komai ya sameshi” Mahaifiyarmu ta gyada mishi kai tana mayar mishi da martanin murmushinsa ta ce, “nima ka rikemun Babana da kyau, kar ka bar wani abun cutarwa ya cutarmun da shi, ka yi tukinka cikin nutsuwa da kiyaye hakkokin hanya karka damu da nasarar da zanyi a kanka” Mahaifinmu ya na murmushi ya amsa mata da cewa, “insha Allah” Nikuwa idanuna suna kan Umar mun kurawa juna ido bama ko kiftawa, sai murmushi ya ke yi mun yana nunamun alamun kar na fadawa Mahaifinmu cewar ba shi ba ne ba har muka rabu suka shiga motarsu, muka shiga motarmu ni da Mahaifina mai gadi ya bude mana gate muka fita. lokacin da muka fito daga cikin gidan ba kowa a kan titin na Mai Ibrahim Road shi ya ba iyayenmu damar kara gudun motocinsu, muka mika a kan titin suna tafiya da gudu tamkar zasu tashi sama, gewaye sukayi basu hau babban titinba kasancewar basa son su hau titin da ya ke da yawan motoci shiyasa suka sauka daga kan titin Mai Ibrahim suka hau ta Damboa Road inda nanma suka sauka muka mika a kan titin Shehu Laminu way, a daidai Post Office round abound ne Mahaifiyarmu da Umar suka mike Maiduguri Road yayin da Mahaifinmu ya karya kwana muka hau titin Ahmadu Bello Way wanda shi ne titin da zai kaimu kasuwar Monday Market ta Maiduguri. Mun dan yi nisa a kan titin muna gudu sannan Mahaifinmu ya lura motar Mahaifiyarmu bata biye da mu kamar yadda ya tsammata don haka ya rage gudun motar sannan ya samu waje ya juya muka koma domin mu bi bayansu ya sanar da ita cewar Monday Market zamuje domin ya manta bai fada mata wacce kasuwa za a je ba. bamu dauki wani lokaci ba muka koma post office roundabout inda Mahaifina ya karya kwanar Maiduguri Road titin da muka ga Mahaifiyata da Umar sun bi. Mai zai faru? Bamuyi nisa da fara tafiya a kan titin ba muka fara jiyo karar harbin bindiga ta ko’ina wanda hakan ya tabbatar mana da harbe-harbe ake a kan titin. Ba tsoro bare fargaba haka Mahaifina ya kara take totur din motarsa muka tunkari wajen da muke jiyo harbin bindigar. “Ya Salam… inna lillahi wa’inna ilaihirraji’un” Ita ce kalmar da na ji Mahaifina yana ta maimaitawa ga wani gumi da ya fara karyo mishi duk da sanyin AC dake ratsamu a cikin motar. tun daga nesa muka hango Motar Mahaifiyata a 22 (ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA BIYU, NA NURA ISA S GARO)tsaye a kan titi da wasu mutane fuskokinsu a lullu6e sun kewaye motar da wasu manya manyan bindigu a hannunsu suna harbin motar ta ko’ina ba tare da sun kakkautaba. Gunjin hargowar tahowar motarmu da suka jiyo ne ya sa suka waigo kanmu a tare suka sassaita bindigoginsu a kanmu amman batare da sun harbemu ba sai mukaga sun juya a guje suka shishshige cikin daji. Mahaifina yana karasawa ya taka birki da karfi wanda ya sa motarmu ta yi wani irin kara saboda yanayin gudun da ya ke. da kyar ta tsaya domin har sai da ya ja hand break wanda ya sa motar juyawa lokaci daya ba shiri. Da gudu muka fita a tare ni da Mahaifina muka tunkari wajen da motar ke tsaye kallo daya za ka yi mana ka fahimci bama cikin hayyacinmu, Mahaifina kuwa jikinsa har rawa ya ke, ya zame ya fadi, na yi saurin karasawa wajensa na kama hannunshi na taimaka mishi ya mike sannan muka karasa wajen motar Mahaifina ya wuce mazaunin direba inda Mahaifiyarmu ke zaune ni kuma na bude 6angaren da Umar ke zaune wanda ina bude murfin motar ya taho zai fado kasancewar a jikin murfin ya jingina na tareshi da hannayena sannan na tallafoshi na kwantar da shi a kan kirjina. Duk mai imani in ya ga yanayin da Umar da Mahaifiyarmu suke dole ya zubar musu da hawaye domin harsashen da ke jikin Umar kadai ban san iyakarsuba. Da kyar ya bude idonsa muna hada ido ya kuramun ido yana kallona sannan ya bude baki yana son yimun magana amman ya kasa saboda halin da ya ke ciki ya munana. Wasu zafafan hawaye ne sukai tsartuwa daga cikin tagwayen idanuna na fashe da kuka mai karfi na bude bakina da zummar na kira sunanshi. “Uma…” Hannun Umar na ga ya sa ya toshemun bakina ya hanani ambaton sunansa, na kalleshi cikin mamaki a lokacin na ga wani tattausan murmushi ya bayyana a kan fuskarsa sai kuma na ga idanunsa sun kakkafe ya kurawa sama ido baya ko kiftawa. “inna lillahi’wa’inna ilaihirraji’un” Ita ce kalmar da na furta domin duk da karancin shekaruna na san Umar ya rasu ya bar duniya kuma bazai kuma dawowaba kenan har abada. “la’ila ha illallah, Muhammadurrasulullah” 23 (ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA BIYU, NA NURA ISA S GARO)Na tsinci muryar Mahaifiyata tana furta kalmar shahada wacce ta zamo kalmarta ta karshe a duniya. Da sauri na daga kai na kalleta sai a lokacin na ga yadda ‘yan bindigar sukai fata-fata da jikinta tana rungume a jikin Mahaifina ya kura mata ido yana kallonta baya iya komai sai zubar da hawaye. Mun dade a haka ina rike da Umar yayin da Mahaifina ke rike da Mahaifiyata, mun yi shiru ba mai iya magana a cikinmu, kukanma da muke mun daina sai alamun bushashshen hawayen da ke kan fuskokinmu. Ba zan iya kididdige tsayin lokacin da muka dauka a haka ba sannan Mahaifina ya yunkura ya dauki gawar Mahaifiyata ya doshi motar da muka zo da ita ya bude bayan motar ya sakata sannan ya dawo ya dauki gawar Umar ya kaita kusa da ta Mahaifiyata ya kwantar da shi, muka mayar da kofofin muka shiga motar muka kama hanyarmu ta komawa gida. Tafiya kawai muke amman babu mai iya magana a cikinmu, bama a zancen kuka domin ya dade da gushewa daga garemu, mun fauwalawa Allah lamuranmu domin shi kadai ya san halin kunci da bakin cikin da wadannan mutane da suka rabamu da masoyanmu suka jefamu. “Allah mai girma!, mai iko akan dukkan bayinsa, mai yin yadda ya so kuma a lokacin da ya so” Mahaifina ya ce cikin wata sassanyar murya mai ban tausayi lokacin da ya ke karya kwanar unguwarmu domin wani bakin hayaki da ya ga ya gauraye layin har baya ganin gabansa sosai, ga jama’a sai guje-guje suke da gawarwaki rike a hannayensu. gidaje duk a rurrushe wanda hakan ya tabbatar mana da irin 6arnar da maharan sukai a cikin unguwar. Mai zai faru? Lokacin da muka karasa kofar gidanmu abun sai ya kara munana a garemu domin yadda muka ga gidan ya ruguje gaba daya alamun da suka tabbatar mana da an jefo bom ko makamancinsa a gidan, katangar gaba daya ta rushe ko’ina ya zama hanya. dakuna biyu ne basu rushe ba a gidan wanda duk da ban shaidasu sosaiba na san dakin Mahaifinmu ne sai kuma dakinmu ni da marigayin Dan uwana Husain. “Ya Salam…” Mahaifina ya ce lokacin da ya ke tsayar da motar a kofar gidan, sannan da sauri ya fita nima na fita daga cikin motar na rufa mishi baya, muna shiga 24 (ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA BIYU, NA NURA ISA S GARO)kai tsaye 6angaren gidan Yayansa muka dosa Alhaji Lawan muka tarar da ana ta kokarin zakuloshi shi da iyalinsa daga karkashin kasa domin ginin da ya rushe ya dannesu. Mahaifina kasa yin komai ya yi domin a kan idonsa muna zuwa aka dago gawar Yayansa a karkashin wani kankaren siminti ya danneshi. Muka samu waje daya muka tsaya tare da zuwaba jama’ar da ke ta famar aikin ceto ido muna kallonsu ni da Mahaifina babu mai magana a cikinmu. Tsawon awa daya muka kwashe a tsaye jama’a na aikin nema sannan aka samo gawar Rufaida ‘yar Yayan Mahaifinmu ita da Mahaifiyarta duk sun mutu babu mai rai a cikinsu. da taimakon jama’ar unguwa muka hadu akai musu wanka da jana’iza sannan aka haka kabarurruka a cikin da’irar rushashshen gidan aka binnesu gaba daya har da gawar Mahaifiyata da ta Umar Dan uwana. ba zancen zaman makoki domin kusan duk rabin unguwar ba inda ba a yi mutuwa ba saboda harin da aka kawo ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, kusan rabin mutanen unguwar duk sun mutu. Inajin kan tarhon gidanmu da ke ajje a dakin Mahaifinmu yana ringi amman ni ko Mahaifina ba wanda ya iya dauka domin bama iya magana, ko magana ka yiwa Mahaifina sai dai ya dagawa mutum kai, ko ya nuna mishi alama da hannu, abinci kuwa da kyar wani makwabcinmu abokin Yayan Babana mai suna Alhaji Sulaiman ya takurawa Mahaifina ya ci nima ya bani a baki na ci kadan na ce na koshi. Alhaji Sulaiman wanda shima gidansa ya rushe gaba daya, duk ‘Ya’yansa sun mutu, daga shi sai matarsa suka rage basu mutuba. Haka rayuwarmu ta kasance a cikin garin Maiduguri tsawon kwana uku duk garin ya yi mana zafi. Mahaifina bai nemi sauran ‘yan uwansaba domin labari ya dade da samunshi cewar unguwar da danginsa suke bawanda ya rayu domin bayan ruwan bama baman da maharan sukayi sai kuma suka shiga cikin garin da bindigogi suka dunga karasa wadanda basu mutuba da wadanda suka ji raunuka. A kwana na ukunne Mahaifina ya ji bazai iya rayuwa a garin Maiduguri ba don haka ya shiga cikin dakinsa ina biye da shi a gefensa, ya dauki wata katuwar jaka da ya ke zuba gwala-gwalai a ciki, ya dauki wata jakar ya debar mana kayan da 25 (ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA BIYU, NA NURA ISA S GARO)zamuyi amfani da su ni da shi, ya dauki kudadansa muka fito wajen da ya ajje motarsa ya bude boat ya zuba kayan sannan muka shiga cikin motar muna kokarin tafiya ne Alhaji Sulaiman da matarsa suka karaso wajen ya tsayar da Mahaifina yana tambayarsa ina zai je amman Mahaifina baya iya magana illa binshi da ya ke da ido ba tare da ya ce mishi komai ba, ganin hakanne ya sa Alhaji Sulaiman ya bude bayan motar shi da matarsa suka shiga ya ce da Mahaifina. “mu je duk inda za ka je Mukhtar nima bazan iya zaman garinnan ba. bazan iya rayuwa a garin Maiduguri ba domin duk lokacin da zan kalli gidannan sai na ga kamar ‘ya’yana da suka mutu zasu dawo” Mahaifina ya ja mota muka tafi a lokacin shi kanshi bai san ina zai je ba, haka ya saita sitiyarin motarsa a kan titin kano bamu tsaya a ko’ina ba duk nisan Maiduguri sai da muka zo garin Kano. Kasancewar Mahaifina ba ya iya yin magana shiyasa muna zuwa kano ya tsayar da motar ya bude boat ya debo kudi masu yawa ya ba Alhaji Sulaiman sannan ya nuna mishi alamar ya sayi gida. Haka kuwa akayi Alhaji Sulaiman ya nemo dillalai suka nuna mana samfuran gidaje daban daban daga karshe Mahaifina ya za6i gidan da ke Sharada Phase I kasancewar gidan ya babbane mai dauke da 6angare uku, sannan unguwar ba mutane sosai akwai karancin hayaniya. Alhaji Sulaiman ya biya kudin da Mahaifina ya bayar sannan Mahaifina ya kara bashi wasu kudin muka shiga kasuwa aka sayo kayayyakin da za a zuba a cikin gidan zuwa kayan abincin da zamu bukata, muka koma gidan Mahaifina ya za6i 6angare daya, Alhaji Sulaiman da Matarsa suka dauki daya 6angaren daya kuma 6angaren aka barshi ba komai a cikinsa. muka shiga 6angaren da Mahaifina ya za6amana yayin da Alhaji Sulaiman da Matarsa suka wuce nasu 6angaren. Muna shiga Mahaifina ya ajje jakar gwala gwalai da ta kudin da ta ke rike a hannunsa sannan ya tsayar da ni ya tsugunna a gabana ya kuramun ido muna ‘yar kallon kallo na tsawon wani lokaci, sai kuma na ga wani tattausan murmushi ya bayyana a kan fuskarsa, abun ya ban mamaki domin ban ta6a zaton wani farin cikin zai kuma ziyartar zuciyar Mahaifina ba. ban san lokacin da hawaye suka

THE AUTHOR NURA ISA S GARO

Nura Isa S Garo shall be a world-class Author comparable to any other, engaged in imparting contemporary knowledge, using high skilled and multi-disciplinary approaches, to men and women of all races, as well as generating new ideas and intellectual practices relevant to the needs of its immediate community, Nigeria and the world at large.




The Author
NURA ISA S GARO

26 (ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA BIYU, NA NURA ISA S GARO)fara zarya a kan fuskata ba saboda tausayin Mahaifina da ya kara dabaibaye zuciyata. “ka daina kuka Umar…” Ya so ya firgitani da sunan da ya kirani da shi. “Umar kuma?” a zatona na zaci Umar ya gani ya dawo sai kuma na gane ashe bai san wanda ya ke tare da shi ba domin sun yi canje da Mahaifiyata ya bata Aliyu ya kar6i Umar, bai san cewar ni ne Dansa Aliyu tsaye a gabansa ba Umar shi ne wanda ya mutu aka binneshi ba. Shirun da na yi ne ya sa shi cigaba da magana da cewa, “a rayuwa Ubangiji Allah yakan jarabci mutum ne da abun da ya fi so domin ya gwada karfin imaninsa” Ya dan yi shiru fuskarsa dauke da alamun damuwa sannan ya ci gaba da cewa, “Dana duk da Ubangiji Allah ya rabamu da abun da muka fi kauna a duniya bai cancanci mu bijire mishi ba idan mukai la’akari da irin ni’imar da ya yi mana ya azurtamu da imani da shi da manzonsa annabi Muhammad (S.A.W)” Mahaifina yana zuwa nan a zancensa wasu tagwayen hawaye suka sauka a kan fuskarsa, yayin da murmushin kan fuskarsa ke kara fadada ya ci gaba da magana da cewa, “ya bamu rai da lafiya, ya azurtamu da ni’imarsa, sannan bai daukemu duka ba ya barmu ni da kai, wanda Allah shi kadai ya barwa kansa sanin dalilin rabamu da wadannan masoya namu da ya yi. Ina son kaima ka yi hakuri ka rungumi kaddara da rashin Mahaifiyarka da Dan uwanka kamar yadda nima na dauki rashinta da Dana Aliyu…” Kukan da ya ke ne ya yi karfi lokacin da ya ambaci sunan ‘Aliyu’ da karfi wanda hakan ya kara tabbatarmun da kaunar da Mahaifina ya ke yi mun ta sha bamban da wacce ya ke yiwa Dan uwana Umar duk da shi ya haifemu, kamarmu daya amman shi so daban ya ke a cikin zuciya Allah ya ke halittarsa, suffa ba ta so! Wanda ka ke so shi zaka so har abada har karshen rayuwarka wani bazai ta6a zama madadin wani ba duk irin alaka da kama da junan da za su yi. Na so na fadawa Mahaifina cewar ba Umar ba ne, ni ne dinnan dai dansa mai kaunarsa, Aliyunsa amman dana bude baki zan fada mishi sai na dunga ganin tamkar Umar yana rikemun 27 (ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA BIYU, NA NURA ISA S GARO)baki yana hanani fadamishi. Wannan dalilin ne ya sa duk tsawon shekarun da muka kwashe da Mahaifina ban sanar da shi cewar ni ne Aliyu ba na kar6i sunan dan uwana da ya ke kirana da shi wato ‘Umar Mukhtar’. Mahaifina ya share hawayen kan fuskarsa tare da kuramun ido yana kallon yadda digon hawaye ke sauka daga cikin idanuna zuwa kan fuskata, ba tare da ya yi yunkurin dakatar da ni ba ya ci gaba da yimun jawabinsa mai jan hankali da sa nutsuwa. “mutanen da suka kashemana ‘yan uwa da masoyanmu mutane ne da ke inkarin daukaka kalmar Allah da fadin cewa zasu kafa daular musulunci amman ko mahaukaci ya kalli irin aikinsu yasan ba imani da Allah a cikin zukatansu, suna kashe musulmai yayin da suke sallah, su kashe musulmai yayinda suke barci ko sana’a a wajen kasuwancinsu, suna kashe musulmai yayin da suke tafiya akan hanya. an kirkiresu ne domin cin mutuncin musulmai ana kiransu da suna ‘yan ta’adda a cikin fadin duniya. Wannan shi ne manufar yahudawa domin durkusar da addinin Allah. Inason ka yadda da kaddara Umar ka zamo Da na gari mai biyayya da tabbatar da gaskiya da rikon amana a tsakanin al’umma. Ka zamo mai koyi da kyawawan dabi’un manzon Allah (S.A.W), idan ka yi haka shi ne zaka amsa sunanka Umar Mukhtar!” Na daga mishi kai cikin karfin gwiwa sannan na sa hannu na goge hawayen dake kan fuskata shima na goge mishi nashi. “Allah ya shima albarka ya baka nasara akan dukkan ayyukan alkairin da ka sa a gaba” “ameen” Na amsawa Mahaifina a karon farko na yi magana tun bayan rasuwar Mahaifiyata da Dan uwana. Mahaifina ya kama hannuna ya shigar da ni bandakin sabon gidannamu ya yi mun wanka ya canzamun kaya sannan ya barni zaune a falon gidan shima ya je ya yi wanka ya canza kayan jikinsa. A lokacin ne Alhaji Sulaiman da matarsa suka shigo cikin falon matarsa na dauke da faranti da abinci jere a kai. Da sauri Mahaifinmu ya tashi domin girmamawa ga abokin Yayannashi ya kar6i farantin hannunta yana cewa, 28 (ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA BIYU, NA NURA ISA S GARO) “Alhaji ai da ka kiramu munje can mun ci abincin ba sai kun dauko kun taho nan da shi ba” Kallonshi kawai suka tsaya suna yi da mamaki akan fuskokinsu ganin yana magana har da wani tattausan murmushi da suka kasa fuskantar na mene ne akan fuskarsa. Mahaifina ya ajje farantin abincin a tsakiyar falon sannan ya juyo ya kallesu ya rike hannun Alhaji Sulaiman yana yi musu magana cikin kwantar da murya. “kar ku damu da halin da kuka tarar da ni Alhaji tunda na bar Maiduguri hankalina zaifi kwanciya a nan. Na fauwalawa Allah dukkan al’amarina na dauki kaddarar da ya doramun domin yadda da kaddara na daya daga cikin imani da Allah” Ya kara damke hannun Alhaji Sulaiman da karfi ya ce, “Alhaji kamar yadda Allah ya kaddara mana wannan abu, ina son mu rike junanmu amana mu zama ‘yan uwa mu ci gaba da zama har zuwa lokacin da Allah ya kaddara mana zama a wannan waje” “mun gode Mukhtar, Allah ya saka maka da alkairi ya bamu juriyar rashin da mukayi” Alhaji Sulaiman ya ce mishi cikin karfin zuciya a lokacin idanunsa suka cicciko da kwalla ya sa gefen rigarsa ya goge hawayensa. “ameen” Muka amsa mishi gaba daya sannan muka zauna muka fara cin abincin. Alhaji Sulaiman da matarsa Hafsat suna burgeni domin a cikinsu sai na rasa wanda ya fi wani karfin zuciya. Ga shi dai duk ‘ya’yansu guda biyar sun mutu a wajen harin da aka kawo, sun bar garin Maiduguri sun baro ‘yan Uwansu amman duk sun fauwalawa Allah lamuransu. “Allah ya sa mu cika da imani” Na ce a cikin zuciyata, a lokacin da na sa hannu na debo abincin na fara ci a hankula cikin nutsuwa. Haka muka ci gaba da rayuwarmu a cikin garin Kano, unguwar sharada, bazan ce cikin jin dadi ba domin mun rabu da wani sashe na jin dadin rayuwarmu. Kwananmu talatin a cikin garin Kano Mahaifina ya nemi shawarar Alhaji Sulaiman akan yana son ya shiga kasuwa ya fara kasuwanci da gwala-gwalan da ya zo da su, kasancewar garin Kano gari ne da Allah ya 29 (ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA BIYU, NA NURA ISA S GARO)albarkaceshi da kasuwanci da malamai masana addinin musulunci. Bayan Alhaji Sulaiman ya amince ne Mahaifina Alhaji Mukhtar ya kama hannuna ya sani a cikin mota muka tafi kasuwar Abubakar Rimi dake sabon gari, ya nemi 6angaren masu sayar da gold aka nuna mishi kai tsaye muka wuce shagon da ya ke fuskantarmu wanda shagon ya kasance babu kaya sosai da wani mutum a zaune ya yi tagumi fuskarsa babu fara’a. lokacin da ya ga mun tunkaro shagonsa ya mike tsaye cikin fara’a da sakin fuska ya tsugunna har kasa ya gaishe da Mahaifina duk da a girme ba lallai ba ne Mahaifina ya girmeshi sai dai su yi sa’annin juna. Mahaifina ya amsa mishi cikin sakin fuska tare da sa hannu ya dago shi muka samu waje muka zauna, Mahaifina ya kare mishi kallo ya aminta da nutsuwa da kamunkan mutumin sannan ya fara yi mishi bayani game da abun da ya kawomu kasuwar akan yanasan ya shiga harkar kasuwancin sayar da gwala-gwalai a cikin kasuwar ta Abubakar Rimi. “masha Allah” Mutumin ya ce tare da mikawa Mahaifina hannu sukayi musabiha a karo na biyu sannan ya fara gabatar da kanshi da cewa, “ni sunana Alhaji Adnan, asalina dan Jihar Kebbi ne kasuwanci ne ya kawoni jihar Kano sannan wannan shagon da ka ke gani nawa ne. na ji dadin da ka nemi shawarata kuma insha Allah zan taimaka maka” Mahaifina ya yi murmushi ya ce, “nagode Allah ya saka da alkairi” Alhaji Adnan ya karewa cikin shagonsa kallo sannan ya kalli Mahaifina ya ce, “amman Alhaji ga wata shawara in bazaka damuba, ka fara kawo kayanka ka kasasu a cikin wannan shagon sai mu dunga zama tare kayana daban naka daban domin wannan kasuwar da ka ke gani samun hayar shago sai ka kashe makudan kudi kafun ka samu” Mahaifina ya ce, “nawa ne hayar Alhaji? Ina da kudi ko nawa ne hayar shagon zan iya bayarwa” Alhaji Adnan ya gyada kai da alama ransa bai so abunda Mahaifina ya fada ba ya ce, “amman Alhaji zai dai fi kyau din ko kana da kudin gwanda ka dado kaya mu cika wannan shagon da su yadda kwarjinin kayan zai dunga

No comments:

Post a Comment