Saturday, September 10, 2016

ZAHIRIN KAUNA LITTAFIN NURA S GARO


UNIVERSITY OF INFORMATION TECHNOLOGY KANO

BARKA DA ZUWA SHAFIN LITATTAFAN MARUBUCI NURA ISA S GARO

LITTAFIN ZAHIRIN KAUNA 21 (ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA BIYU, NA NURA ISA S GARO)uwana ya umarceni, Mahaifiyata ta ja hannuna muka doshi wajen da motarta take, Umar da Mahaifinmu suma suka juya zasu inda motar Mahaifinmu take, har sun bude motar zasu shiga Mahaifiyarmu ta canza shawara don haka ta juya ta kalli Mahaifinmu dake kokarin saka Umar a gaban mota ta kira sunanshi cikin sassanyar muryarta. “Alhaji!” Da sauri Mahaifinmu ya juyo ya kalleta da murmushinsa da ba’a rabashi da shi a ko da yaushe ya ce, “na’am Hajiya” Mahaifiyarmu ta kama hannuna muka karasa wajen da Mahaifina da Umar ke tsaye ta mika mishi ni sannan ta sa hannu ta kar6i Umar daga hannunsa ta ce mishi. “yau canji za a yi ka dau Umar ni na dauki Aliyu” Mahaifinmu ya fadada murmushin kan fuskarsa yana kallonta cikin nuna kulawa ya ce, “shikenan Hajiya ammanfa ki rikemun Babana da kyau ki kulamun da shi, kar ki bar komai ya sameshi” Mahaifiyarmu ta gyada mishi kai tana mayar mishi da martanin murmushinsa ta ce, “nima ka rikemun Babana da kyau, kar ka bar wani abun cutarwa ya cutarmun da shi, ka yi tukinka cikin nutsuwa da kiyaye hakkokin hanya karka damu da nasarar da zanyi a kanka” Mahaifinmu ya na murmushi ya amsa mata da cewa, “insha Allah” Nikuwa idanuna suna kan Umar mun kurawa juna ido bama ko kiftawa, sai murmushi ya ke yi mun yana nunamun alamun kar na fadawa Mahaifinmu cewar ba shi ba ne ba har muka rabu suka shiga motarsu, muka shiga motarmu ni da Mahaifina mai gadi ya bude mana gate muka fita. lokacin da muka fito daga cikin gidan ba kowa a kan titin na Mai Ibrahim Road shi ya ba iyayenmu damar kara gudun motocinsu, muka mika a kan titin suna tafiya da gudu tamkar zasu tashi sama, gewaye sukayi basu hau babban titinba kasancewar basa son su hau titin da ya ke da yawan motoci shiyasa suka sauka daga kan titin Mai Ibrahim suka hau ta Damboa Road inda nanma suka sauka muka mika a kan titin Shehu Laminu way, a daidai Post Office round abound ne Mahaifiyarmu da Umar suka mike Maiduguri Road yayin da Mahaifinmu ya karya kwana muka hau titin Ahmadu Bello Way wanda shi ne titin da zai kaimu kasuwar Monday Market ta Maiduguri. Mun dan yi nisa a kan titin muna gudu sannan Mahaifinmu ya lura motar Mahaifiyarmu bata biye da mu kamar yadda ya tsammata don haka ya rage gudun motar sannan ya samu waje ya juya muka koma domin mu bi bayansu ya sanar da ita cewar Monday Market zamuje domin ya manta bai fada mata wacce kasuwa za a je ba. bamu dauki wani lokaci ba muka koma post office roundabout inda Mahaifina ya karya kwanar Maiduguri Road titin da muka ga Mahaifiyata da Umar sun bi. Mai zai faru? Bamuyi nisa da fara tafiya a kan titin ba muka fara jiyo karar harbin bindiga ta ko’ina wanda hakan ya tabbatar mana da harbe-harbe ake a kan titin. Ba tsoro bare fargaba haka Mahaifina ya kara take totur din motarsa muka tunkari wajen da muke jiyo harbin bindigar. “Ya Salam… inna lillahi wa’inna ilaihirraji’un” Ita ce kalmar da na ji Mahaifina yana ta maimaitawa ga wani gumi da ya fara karyo mishi duk da sanyin AC dake ratsamu a cikin motar. tun daga nesa muka hango Motar Mahaifiyata a 22 (ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA BIYU, NA NURA ISA S GARO)tsaye a kan titi da wasu mutane fuskokinsu a lullu6e sun kewaye motar da wasu manya manyan bindigu a hannunsu suna harbin motar ta ko’ina ba tare da sun kakkautaba. Gunjin hargowar tahowar motarmu da suka jiyo ne ya sa suka waigo kanmu a tare suka sassaita bindigoginsu a kanmu amman batare da sun harbemu ba sai mukaga sun juya a guje suka shishshige cikin daji. Mahaifina yana karasawa ya taka birki da karfi wanda ya sa motarmu ta yi wani irin kara saboda yanayin gudun da ya ke. da kyar ta tsaya domin har sai da ya ja hand break wanda ya sa motar juyawa lokaci daya ba shiri. Da gudu muka fita a tare ni da Mahaifina muka tunkari wajen da motar ke tsaye kallo daya za ka yi mana ka fahimci bama cikin hayyacinmu, Mahaifina kuwa jikinsa har rawa ya ke, ya zame ya fadi, na yi saurin karasawa wajensa na kama hannunshi na taimaka mishi ya mike sannan muka karasa wajen motar Mahaifina ya wuce mazaunin direba inda Mahaifiyarmu ke zaune ni kuma na bude 6angaren da Umar ke zaune wanda ina bude murfin motar ya taho zai fado kasancewar a jikin murfin ya jingina na tareshi da hannayena sannan na tallafoshi na kwantar da shi a kan kirjina. Duk mai imani in ya ga yanayin da Umar da Mahaifiyarmu suke dole ya zubar musu da hawaye domin harsashen da ke jikin Umar kadai ban san iyakarsuba. Da kyar ya bude idonsa muna hada ido ya kuramun ido yana kallona sannan ya bude baki yana son yimun magana amman ya kasa saboda halin da ya ke ciki ya munana. Wasu zafafan hawaye ne sukai tsartuwa daga cikin tagwayen idanuna na fashe da kuka mai karfi na bude bakina da zummar na kira sunanshi. “Uma…” Hannun Umar na ga ya sa ya toshemun bakina ya hanani ambaton sunansa, na kalleshi cikin mamaki a lokacin na ga wani tattausan murmushi ya bayyana a kan fuskarsa sai kuma na ga idanunsa sun kakkafe ya kurawa sama ido baya ko kiftawa. “inna lillahi’wa’inna ilaihirraji’un” Ita ce kalmar da na furta domin duk da karancin shekaruna na san Umar ya rasu ya bar duniya kuma bazai kuma dawowaba kenan har abada. “la’ila ha illallah, Muhammadurrasulullah” 23 (ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA BIYU, NA NURA ISA S GARO)Na tsinci muryar Mahaifiyata tana furta kalmar shahada wacce ta zamo kalmarta ta karshe a duniya. Da sauri na daga kai na kalleta sai a lokacin na ga yadda ‘yan bindigar sukai fata-fata da jikinta tana rungume a jikin Mahaifina ya kura mata ido yana kallonta baya iya komai sai zubar da hawaye. Mun dade a haka ina rike da Umar yayin da Mahaifina ke rike da Mahaifiyata, mun yi shiru ba mai iya magana a cikinmu, kukanma da muke mun daina sai alamun bushashshen hawayen da ke kan fuskokinmu. Ba zan iya kididdige tsayin lokacin da muka dauka a haka ba sannan Mahaifina ya yunkura ya dauki gawar Mahaifiyata ya doshi motar da muka zo da ita ya bude bayan motar ya sakata sannan ya dawo ya dauki gawar Umar ya kaita kusa da ta Mahaifiyata ya kwantar da shi, muka mayar da kofofin muka shiga motar muka kama hanyarmu ta komawa gida. Tafiya kawai muke amman babu mai iya magana a cikinmu, bama a zancen kuka domin ya dade da gushewa daga garemu, mun fauwalawa Allah lamuranmu domin shi kadai ya san halin kunci da bakin cikin da wadannan mutane da suka rabamu da masoyanmu suka jefamu. “Allah mai girma!, mai iko akan dukkan bayinsa, mai yin yadda ya so kuma a lokacin da ya so” Mahaifina ya ce cikin wata sassanyar murya mai ban tausayi lokacin da ya ke karya kwanar unguwarmu domin wani bakin hayaki da ya ga ya gauraye layin har baya ganin gabansa sosai, ga jama’a sai guje-guje suke da gawarwaki rike a hannayensu. gidaje duk a rurrushe wanda hakan ya tabbatar mana da irin 6arnar da maharan sukai a cikin unguwar. Mai zai faru? Lokacin da muka karasa kofar gidanmu abun sai ya kara munana a garemu domin yadda muka ga gidan ya ruguje gaba daya alamun da suka tabbatar mana da an jefo bom ko makamancinsa a gidan, katangar gaba daya ta rushe ko’ina ya zama hanya. dakuna biyu ne basu rushe ba a gidan wanda duk da ban shaidasu sosaiba na san dakin Mahaifinmu ne sai kuma dakinmu ni da marigayin Dan uwana Husain. “Ya Salam…” Mahaifina ya ce lokacin da ya ke tsayar da motar a kofar gidan, sannan da sauri ya fita nima na fita daga cikin motar na rufa mishi baya, muna shiga 24 (ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA BIYU, NA NURA ISA S GARO)kai tsaye 6angaren gidan Yayansa muka dosa Alhaji Lawan muka tarar da ana ta kokarin zakuloshi shi da iyalinsa daga karkashin kasa domin ginin da ya rushe ya dannesu. Mahaifina kasa yin komai ya yi domin a kan idonsa muna zuwa aka dago gawar Yayansa a karkashin wani kankaren siminti ya danneshi. Muka samu waje daya muka tsaya tare da zuwaba jama’ar da ke ta famar aikin ceto ido muna kallonsu ni da Mahaifina babu mai magana a cikinmu. Tsawon awa daya muka kwashe a tsaye jama’a na aikin nema sannan aka samo gawar Rufaida ‘yar Yayan Mahaifinmu ita da Mahaifiyarta duk sun mutu babu mai rai a cikinsu. da taimakon jama’ar unguwa muka hadu akai musu wanka da jana’iza sannan aka haka kabarurruka a cikin da’irar rushashshen gidan aka binnesu gaba daya har da gawar Mahaifiyata da ta Umar Dan uwana. ba zancen zaman makoki domin kusan duk rabin unguwar ba inda ba a yi mutuwa ba saboda harin da aka kawo ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, kusan rabin mutanen unguwar duk sun mutu. Inajin kan tarhon gidanmu da ke ajje a dakin Mahaifinmu yana ringi amman ni ko Mahaifina ba wanda ya iya dauka domin bama iya magana, ko magana ka yiwa Mahaifina sai dai ya dagawa mutum kai, ko ya nuna mishi alama da hannu, abinci kuwa da kyar wani makwabcinmu abokin Yayan Babana mai suna Alhaji Sulaiman ya takurawa Mahaifina ya ci nima ya bani a baki na ci kadan na ce na koshi. Alhaji Sulaiman wanda shima gidansa ya rushe gaba daya, duk ‘Ya’yansa sun mutu, daga shi sai matarsa suka rage basu mutuba. Haka rayuwarmu ta kasance a cikin garin Maiduguri tsawon kwana uku duk garin ya yi mana zafi. Mahaifina bai nemi sauran ‘yan uwansaba domin labari ya dade da samunshi cewar unguwar da danginsa suke bawanda ya rayu domin bayan ruwan bama baman da maharan sukayi sai kuma suka shiga cikin garin da bindigogi suka dunga karasa wadanda basu mutuba da wadanda suka ji raunuka. A kwana na ukunne Mahaifina ya ji bazai iya rayuwa a garin Maiduguri ba don haka ya shiga cikin dakinsa ina biye da shi a gefensa, ya dauki wata katuwar jaka da ya ke zuba gwala-gwalai a ciki, ya dauki wata jakar ya debar mana kayan da 25 (ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA BIYU, NA NURA ISA S GARO)zamuyi amfani da su ni da shi, ya dauki kudadansa muka fito wajen da ya ajje motarsa ya bude boat ya zuba kayan sannan muka shiga cikin motar muna kokarin tafiya ne Alhaji Sulaiman da matarsa suka karaso wajen ya tsayar da Mahaifina yana tambayarsa ina zai je amman Mahaifina baya iya magana illa binshi da ya ke da ido ba tare da ya ce mishi komai ba, ganin hakanne ya sa Alhaji Sulaiman ya bude bayan motar shi da matarsa suka shiga ya ce da Mahaifina. “mu je duk inda za ka je Mukhtar nima bazan iya zaman garinnan ba. bazan iya rayuwa a garin Maiduguri ba domin duk lokacin da zan kalli gidannan sai na ga kamar ‘ya’yana da suka mutu zasu dawo” Mahaifina ya ja mota muka tafi a lokacin shi kanshi bai san ina zai je ba, haka ya saita sitiyarin motarsa a kan titin kano bamu tsaya a ko’ina ba duk nisan Maiduguri sai da muka zo garin Kano. Kasancewar Mahaifina ba ya iya yin magana shiyasa muna zuwa kano ya tsayar da motar ya bude boat ya debo kudi masu yawa ya ba Alhaji Sulaiman sannan ya nuna mishi alamar ya sayi gida. Haka kuwa akayi Alhaji Sulaiman ya nemo dillalai suka nuna mana samfuran gidaje daban daban daga karshe Mahaifina ya za6i gidan da ke Sharada Phase I kasancewar gidan ya babbane mai dauke da 6angare uku, sannan unguwar ba mutane sosai akwai karancin hayaniya. Alhaji Sulaiman ya biya kudin da Mahaifina ya bayar sannan Mahaifina ya kara bashi wasu kudin muka shiga kasuwa aka sayo kayayyakin da za a zuba a cikin gidan zuwa kayan abincin da zamu bukata, muka koma gidan Mahaifina ya za6i 6angare daya, Alhaji Sulaiman da Matarsa suka dauki daya 6angaren daya kuma 6angaren aka barshi ba komai a cikinsa. muka shiga 6angaren da Mahaifina ya za6amana yayin da Alhaji Sulaiman da Matarsa suka wuce nasu 6angaren. Muna shiga Mahaifina ya ajje jakar gwala gwalai da ta kudin da ta ke rike a hannunsa sannan ya tsayar da ni ya tsugunna a gabana ya kuramun ido muna ‘yar kallon kallo na tsawon wani lokaci, sai kuma na ga wani tattausan murmushi ya bayyana a kan fuskarsa, abun ya ban mamaki domin ban ta6a zaton wani farin cikin zai kuma ziyartar zuciyar Mahaifina ba. ban san lokacin da hawaye suka

THE AUTHOR NURA ISA S GARO

Nura Isa S Garo shall be a world-class Author comparable to any other, engaged in imparting contemporary knowledge, using high skilled and multi-disciplinary approaches, to men and women of all races, as well as generating new ideas and intellectual practices relevant to the needs of its immediate community, Nigeria and the world at large.




The Author
NURA ISA S GARO

26 (ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA BIYU, NA NURA ISA S GARO)fara zarya a kan fuskata ba saboda tausayin Mahaifina da ya kara dabaibaye zuciyata. “ka daina kuka Umar…” Ya so ya firgitani da sunan da ya kirani da shi. “Umar kuma?” a zatona na zaci Umar ya gani ya dawo sai kuma na gane ashe bai san wanda ya ke tare da shi ba domin sun yi canje da Mahaifiyata ya bata Aliyu ya kar6i Umar, bai san cewar ni ne Dansa Aliyu tsaye a gabansa ba Umar shi ne wanda ya mutu aka binneshi ba. Shirun da na yi ne ya sa shi cigaba da magana da cewa, “a rayuwa Ubangiji Allah yakan jarabci mutum ne da abun da ya fi so domin ya gwada karfin imaninsa” Ya dan yi shiru fuskarsa dauke da alamun damuwa sannan ya ci gaba da cewa, “Dana duk da Ubangiji Allah ya rabamu da abun da muka fi kauna a duniya bai cancanci mu bijire mishi ba idan mukai la’akari da irin ni’imar da ya yi mana ya azurtamu da imani da shi da manzonsa annabi Muhammad (S.A.W)” Mahaifina yana zuwa nan a zancensa wasu tagwayen hawaye suka sauka a kan fuskarsa, yayin da murmushin kan fuskarsa ke kara fadada ya ci gaba da magana da cewa, “ya bamu rai da lafiya, ya azurtamu da ni’imarsa, sannan bai daukemu duka ba ya barmu ni da kai, wanda Allah shi kadai ya barwa kansa sanin dalilin rabamu da wadannan masoya namu da ya yi. Ina son kaima ka yi hakuri ka rungumi kaddara da rashin Mahaifiyarka da Dan uwanka kamar yadda nima na dauki rashinta da Dana Aliyu…” Kukan da ya ke ne ya yi karfi lokacin da ya ambaci sunan ‘Aliyu’ da karfi wanda hakan ya kara tabbatarmun da kaunar da Mahaifina ya ke yi mun ta sha bamban da wacce ya ke yiwa Dan uwana Umar duk da shi ya haifemu, kamarmu daya amman shi so daban ya ke a cikin zuciya Allah ya ke halittarsa, suffa ba ta so! Wanda ka ke so shi zaka so har abada har karshen rayuwarka wani bazai ta6a zama madadin wani ba duk irin alaka da kama da junan da za su yi. Na so na fadawa Mahaifina cewar ba Umar ba ne, ni ne dinnan dai dansa mai kaunarsa, Aliyunsa amman dana bude baki zan fada mishi sai na dunga ganin tamkar Umar yana rikemun 27 (ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA BIYU, NA NURA ISA S GARO)baki yana hanani fadamishi. Wannan dalilin ne ya sa duk tsawon shekarun da muka kwashe da Mahaifina ban sanar da shi cewar ni ne Aliyu ba na kar6i sunan dan uwana da ya ke kirana da shi wato ‘Umar Mukhtar’. Mahaifina ya share hawayen kan fuskarsa tare da kuramun ido yana kallon yadda digon hawaye ke sauka daga cikin idanuna zuwa kan fuskata, ba tare da ya yi yunkurin dakatar da ni ba ya ci gaba da yimun jawabinsa mai jan hankali da sa nutsuwa. “mutanen da suka kashemana ‘yan uwa da masoyanmu mutane ne da ke inkarin daukaka kalmar Allah da fadin cewa zasu kafa daular musulunci amman ko mahaukaci ya kalli irin aikinsu yasan ba imani da Allah a cikin zukatansu, suna kashe musulmai yayin da suke sallah, su kashe musulmai yayinda suke barci ko sana’a a wajen kasuwancinsu, suna kashe musulmai yayin da suke tafiya akan hanya. an kirkiresu ne domin cin mutuncin musulmai ana kiransu da suna ‘yan ta’adda a cikin fadin duniya. Wannan shi ne manufar yahudawa domin durkusar da addinin Allah. Inason ka yadda da kaddara Umar ka zamo Da na gari mai biyayya da tabbatar da gaskiya da rikon amana a tsakanin al’umma. Ka zamo mai koyi da kyawawan dabi’un manzon Allah (S.A.W), idan ka yi haka shi ne zaka amsa sunanka Umar Mukhtar!” Na daga mishi kai cikin karfin gwiwa sannan na sa hannu na goge hawayen dake kan fuskata shima na goge mishi nashi. “Allah ya shima albarka ya baka nasara akan dukkan ayyukan alkairin da ka sa a gaba” “ameen” Na amsawa Mahaifina a karon farko na yi magana tun bayan rasuwar Mahaifiyata da Dan uwana. Mahaifina ya kama hannuna ya shigar da ni bandakin sabon gidannamu ya yi mun wanka ya canzamun kaya sannan ya barni zaune a falon gidan shima ya je ya yi wanka ya canza kayan jikinsa. A lokacin ne Alhaji Sulaiman da matarsa suka shigo cikin falon matarsa na dauke da faranti da abinci jere a kai. Da sauri Mahaifinmu ya tashi domin girmamawa ga abokin Yayannashi ya kar6i farantin hannunta yana cewa, 28 (ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA BIYU, NA NURA ISA S GARO) “Alhaji ai da ka kiramu munje can mun ci abincin ba sai kun dauko kun taho nan da shi ba” Kallonshi kawai suka tsaya suna yi da mamaki akan fuskokinsu ganin yana magana har da wani tattausan murmushi da suka kasa fuskantar na mene ne akan fuskarsa. Mahaifina ya ajje farantin abincin a tsakiyar falon sannan ya juyo ya kallesu ya rike hannun Alhaji Sulaiman yana yi musu magana cikin kwantar da murya. “kar ku damu da halin da kuka tarar da ni Alhaji tunda na bar Maiduguri hankalina zaifi kwanciya a nan. Na fauwalawa Allah dukkan al’amarina na dauki kaddarar da ya doramun domin yadda da kaddara na daya daga cikin imani da Allah” Ya kara damke hannun Alhaji Sulaiman da karfi ya ce, “Alhaji kamar yadda Allah ya kaddara mana wannan abu, ina son mu rike junanmu amana mu zama ‘yan uwa mu ci gaba da zama har zuwa lokacin da Allah ya kaddara mana zama a wannan waje” “mun gode Mukhtar, Allah ya saka maka da alkairi ya bamu juriyar rashin da mukayi” Alhaji Sulaiman ya ce mishi cikin karfin zuciya a lokacin idanunsa suka cicciko da kwalla ya sa gefen rigarsa ya goge hawayensa. “ameen” Muka amsa mishi gaba daya sannan muka zauna muka fara cin abincin. Alhaji Sulaiman da matarsa Hafsat suna burgeni domin a cikinsu sai na rasa wanda ya fi wani karfin zuciya. Ga shi dai duk ‘ya’yansu guda biyar sun mutu a wajen harin da aka kawo, sun bar garin Maiduguri sun baro ‘yan Uwansu amman duk sun fauwalawa Allah lamuransu. “Allah ya sa mu cika da imani” Na ce a cikin zuciyata, a lokacin da na sa hannu na debo abincin na fara ci a hankula cikin nutsuwa. Haka muka ci gaba da rayuwarmu a cikin garin Kano, unguwar sharada, bazan ce cikin jin dadi ba domin mun rabu da wani sashe na jin dadin rayuwarmu. Kwananmu talatin a cikin garin Kano Mahaifina ya nemi shawarar Alhaji Sulaiman akan yana son ya shiga kasuwa ya fara kasuwanci da gwala-gwalan da ya zo da su, kasancewar garin Kano gari ne da Allah ya 29 (ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA BIYU, NA NURA ISA S GARO)albarkaceshi da kasuwanci da malamai masana addinin musulunci. Bayan Alhaji Sulaiman ya amince ne Mahaifina Alhaji Mukhtar ya kama hannuna ya sani a cikin mota muka tafi kasuwar Abubakar Rimi dake sabon gari, ya nemi 6angaren masu sayar da gold aka nuna mishi kai tsaye muka wuce shagon da ya ke fuskantarmu wanda shagon ya kasance babu kaya sosai da wani mutum a zaune ya yi tagumi fuskarsa babu fara’a. lokacin da ya ga mun tunkaro shagonsa ya mike tsaye cikin fara’a da sakin fuska ya tsugunna har kasa ya gaishe da Mahaifina duk da a girme ba lallai ba ne Mahaifina ya girmeshi sai dai su yi sa’annin juna. Mahaifina ya amsa mishi cikin sakin fuska tare da sa hannu ya dago shi muka samu waje muka zauna, Mahaifina ya kare mishi kallo ya aminta da nutsuwa da kamunkan mutumin sannan ya fara yi mishi bayani game da abun da ya kawomu kasuwar akan yanasan ya shiga harkar kasuwancin sayar da gwala-gwalai a cikin kasuwar ta Abubakar Rimi. “masha Allah” Mutumin ya ce tare da mikawa Mahaifina hannu sukayi musabiha a karo na biyu sannan ya fara gabatar da kanshi da cewa, “ni sunana Alhaji Adnan, asalina dan Jihar Kebbi ne kasuwanci ne ya kawoni jihar Kano sannan wannan shagon da ka ke gani nawa ne. na ji dadin da ka nemi shawarata kuma insha Allah zan taimaka maka” Mahaifina ya yi murmushi ya ce, “nagode Allah ya saka da alkairi” Alhaji Adnan ya karewa cikin shagonsa kallo sannan ya kalli Mahaifina ya ce, “amman Alhaji ga wata shawara in bazaka damuba, ka fara kawo kayanka ka kasasu a cikin wannan shagon sai mu dunga zama tare kayana daban naka daban domin wannan kasuwar da ka ke gani samun hayar shago sai ka kashe makudan kudi kafun ka samu” Mahaifina ya ce, “nawa ne hayar Alhaji? Ina da kudi ko nawa ne hayar shagon zan iya bayarwa” Alhaji Adnan ya gyada kai da alama ransa bai so abunda Mahaifina ya fada ba ya ce, “amman Alhaji zai dai fi kyau din ko kana da kudin gwanda ka dado kaya mu cika wannan shagon da su yadda kwarjinin kayan zai dunga

Thursday, September 8, 2016

LITTAFIN ZAHIRIN KAUNA NA DAYA 16 to 20


ZAHIRIN KAUNA
Nura Isa S Garo

16(ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA DAYA, NA NURA S GARO) “shin ko mece ce hujjarka ta cewa [anka bai turomu wajenka domin muyi narasa a cikin wannan shari’a ba, duk da makudan kudin da ya bayar da irin kuka da tashin hankalin da ya shiga lokacin da ya ji labarin an kamaka ka aikata wannan laifi?” Alhaji Mukhtar ya yi murmushi wanda har sai da fararen hakoran da ke jere a cikin dasashin bakinsa suka bayyana. Ya ce, “tambayarki bata yi daidai da irin tambayoyin da ya kamata a ce kinamunba ‘yata, amman domin na cire muku dukkan wani shakku daga cikin zuciyarku yana da kyau na sanar muku” Ya danyi shiru yayinda murmushin kan fuskarsa ya dauke, ya mayar da hankalinsa gaba daya kan Barrister Halima sannan ya ci gaba da magana cikin nutsuwa, “Allah Ubangijin da ya halicci sammai da kassai shi ya fi sona fiye da kowa, sai manzonmu Annabi Muhammad (S.W.A), ina tabbatar miki na ukun shi ne Umar Mukhtar. Yana bala’in sona fiye da yadda bakina zai furta miki Barrister, zai iya bada rayuwarsa domin ya fanshi raina saboda irin kaunar da ya ke yi mun. na ba shi tarbiya irinta addinin musulunci don haka ba zai ta6a goyan bayana akan laifin kisan kaiba sai dai ya dauki wannan laifi nawa a matsayin wata jarrabawa daga cikin jarrabawon Ubangijinsa, rabani da shi ba karamar jarrabawa ba ce a gareshi domin ba shi da kowa sai ni” Barrister Zahra da Barrister Halima suka yi ajiyar zuciya a lokaci daya yayinda tausayin Umar ya kara dabaibaye zuciyarta ta kalli Alhaji Mukhtar ta ce, “Alhaji ko zaka iya yi mana bayani akan yadda wannan lamari ya kasance da kai tun daga lokacin da kai furucin zaka kashe ‘yar Alhaji Adnan wato Suhailat zuwa lokacin da ka daki motarta ta yi hatsari?” Alhaji Mukhtar ya kalli Barrister Zahra ya ce, “hakan ta faru ne lokacin da [ana ya kirani ya ke sanar da ni cewar Alhaji Adnan ya ce bazai ba shi auren ‘yarsaba. A lokacin da na yi amfani da wannan hadisin na manzon Allah (S.A.W) da sahabinsa yake cemishi ka bani shawara manzon Allah ya ke cemishi kar ka yi fushi har sau uku da duk haka bata faruba. Domin kuwa muna gama waya da Umar na kasa zaune na kasa tsaye har sai da zuciyata ta rayamun na je har gidan su Suhailat na yi mata barazana da zan kasheta ko za ta ji tsoran mutuwa ta amince da auren Umar. Hakan kuwa akai na fita daga gida ban zame ko ina ba sai gidan Alhaji Adnan inda na same su a falon gidansa shi da matarsa da ‘yarsa na fadi abunda ke cikin zuciyata. Duk sun tsorata da jin kalamaina inda na tafi na barsu cikin zulumi. Kwana hudu da faruwar hakan ina cikin tafiya a motata kawai sai ji na yi na daki mota wacce nan ta ke ta fada cikin kwalbatin magudanar ruwan da akayi domin wucewar ruwa. Hankalina a tashe na fito mutane suka taimakamun aka fito da su aka sa su a motata na kaisu asibiti. Hankalina ya yi bala’in tashi a lokacin duk na rude ban gane wace ce ba duk da daman ba wani saninta na yi ba domin ganin farko da na yi mata shi ne lokacin da na je har gidansu na ce zan kasheta. ban tashi gane cewar Suhailat Adnan ba ce sai da Mahaifinta da Mahaifiyarta suka shigo cikin asibitin hankalinsu a tashe Mahaifiyar yarinyar tana kuka” 17(ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA DAYA, NA NURA S GARO) Alhaji Mukhtar Maidugu ya yi shiru tare da yin wata bayyananniyar ajiyar zuciya sannan ya ci gaba da cewa, “na shiga halin rudu da danasanin furucina a lokacin da ba shi da amfani, nasan bawanda zai yarda cewar ba da sanina na daki motar Suhailat ba, har [ana Umar baya goyan bayana domin yana kafa hujja da cewar duk abunda na ce zanyi sai na yi shi ko mene ne. ni kaina ba zan iya gaskata kaina ba Barrister” Barrister Zahra da Halima suka yi shiru sun nutsu suna sauraronsa har ya kai karshen bayanin da ya ke musu sannan Barrister Zahra ta ce, “mun gode da hadin kan da ka bamu, gobe insha Allah zamu hadu a kotu” “Allah ya kaimu” Alhaji Mukhtar ya ce tare da yi musu sallama sannan ya juya ya koma inda ya taso ya zauna ya ci gaba da lazimi da ambaton Allah kamar yadda suka zo suka tarar da shi. Barrister Halima ta kama hannun Barrister Zahra suka juya suka fita daga cikin jerin dakunan kurkukun. “yanzu kuma sai ina kenan?” Barrister Halima ce ta tambayi Barrister Zahra lokacin da suke kokarin fita daga cikin wajen. “sashen tattara bayanai zamu shiga domin duba irin bayanan da ‘yan sanda suka yi a kan yadda hatsarin ya faru” Barrister Zahra ta bata amsa a lokacin da suka tsaya a kofar shiga ofishin da ta ke fada. “hakan ya yi kyau” Barrister Halima ta ce sannan ta sa hannu ta bude kofar suka tura kai suka shiga sashen ‘yan sandan da ke sashen suka dunga gaishe da su suna amsawa cikin sakin fuska. Kai tsaye 6angaren babban jami’in da ke kula da shiyyar suka zarce wanda suka sameshi ya dukufa sai aikin rubuce rubuce ya ke kamar yadda ya saba, bayan sun yi mishi sallama ne ya amsa cikin sakin fuska yana murmushi ya mike tsaye domin girmamawa ga manyan lauyoyin guda biyu sannan ya basu waje suka zauna. “muna son bayanan da kuka dauka akan hatsarin da ya afku tsakanin Alhaji Mukhtar Mai Gaskiya da Suhailat Adnan” Barrister Zahra ta yi saurin yi mishi magana lokacin da suka zauna domin gajarce lokutan da suke 6atawa a duk sashen da suka shiga. Jami’in ya yi saurin jan Computer da ke gabansa ya fara daddannawa bayan wani dan lokaci ya binciko bayanan da ke ajje a cikin computar ya buga a takardu ya mika musu sannan ya dauko hotunan motar da akai hatsarin tare da hotunan Suhailat da aka dauketa tun daga asibitin har zuwa gida da inda aka sata a kabari ya mika musu suka kar6a suna duddubawa cikin nutsuwa. Bayan sun gama duddubawa ne Barrister Halima ta kalli Jami’in mai suna ASP Ibrahim ta ce, 18(ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA DAYA, NA NURA S GARO) “Ibrahim zamu tafi da wadannan hotunan domin kara nazari da bincike a kansu” “bakomai Hajiya daman mallakarsu yana da amfani” ASP Ibrahim ya bata amsa sannan ta bude cikin jakar da ke ajje a kan cinyarta ta saka hotan ta daga kanta ta kalli Jami’in dan sandan ta ci gaba da cewa, “a hannun wa case dinnan kuwa ya ke Ibrahim?” “ASP Mubarak Ameen” Ibrahim ya bata amsar tambayar da ta yi mishi tare da kara nutsuwa domin ya san a ko da yaushe za ta iya yi mishi wata domin yasan halinsu ne na lauyoyi. Barrister Halima ta gyada kai cikin gamsuwa da amsar da ASP Ibrahim ya bata sannan ta ce, “wanne likita ne ya aunata ya tabbatar da cewar ta mutu?” “Doctor Kabeer Abdullahi” “Ya salam…” Barrister Zahra ta ce cikin sauri tare da dafe kanta da hannayenta bibbiyu saboda sara matan da ta ji ya yi lokaci tsaya. “lafiya Barrister?” ASP Ibrahim ya tambayeta a hanzarce tare da mayar da hankalinsa kanta. “bakomi Ibrahim kaina na ji ya fara sarawa bana jin dadi sosai” Barrister Zahra ta ba shi amsa tana dan yatsina fuska don kar jami’in dan sandan ya fahimci halin rudanin da ta shiga tun gabannin jin sunan ASP Mubarak da Doctor Kabeer a cikin case din. Barriser Halima da tuni ta gama fahimtar halin da aminiyartata ta shiga ta kalleta a hankalce ta ce, “ko dai sai kin kara shan magananin nan ne Barrister?” “ina kyautata zaton haka sai dai kuma na mantoshi a mota in mun fita na sha” Barrister Zahra ta bata amsa. “Allah ya sauwake, ya baki lafiya” ASP Ibrahim ya ce fuskarsa na nuna alamun tausayi. “ameen” Suka amsa gaba dayansu sannan Barrister Halima ta kalleshi ta ce, 19(ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA DAYA, NA NURA S GARO) “to mungode ASP zamu tafi sai mun kara waiwayarka kenan idan bukatar hakan ta taso” “shikenan Hajiya nagode Allah ya saka da alkairi” ASP Ibrahim ya ce mata a lokacin da suka mike, Barrister Halima ta rataya jakarta a kafada sannan ta kama hannun Barrister Zahra wacce ta kasa yin magana, suka juya suka fita ASP Ibrahim ya bisu da kallo har sai da suka fita daga cikin sashen tattara bayanan sannan ya yi ajiyar zuciya ya dukufar da kai ya ci gaba da yin aikinsa. Fitarsu daga cikin sashen bincikar masu manyan laifuffukan na bompai ke da wuya suka shiga motarsu, Barrister Halima ta kar6i tukin kasancewar ta fahimci hankalin kawartata ya yi matukar tashi wanda a matsayinsu na masana doka tasan doka bata yarda mutum ya yi tukin mota a cikin irin wannan halin ba. Sai da Barrister Halima ta saita kan sitiyarin motar a kan titin Hadejia Road daura da Wellcare Kano sannan ta juya ta kalli Barrister Zahra a nutse ta fara yi mata magana cikin nutsuwa. “na fahimci kin tayar da hankalinki da yawa Barrister, kar ki manta shari’a sa6anin hankali ce ba duk abun da mutum ke zargi ba ne ya ke kasance gaskiya” Barrister Zahra ta yi wata bayyananniyar ajiyar zuciya ta kalli Barrister Halima ta ce, “abun ne ya ke bani tsoro Halima, a ce duk wanda case dinnan ke hannunsa mutumin kirki ne, jajirtacce ne, sannan mai kokarin ganin ya tabbatar da gaskiya ne. Kai hatta Alhaji Mukhtar da ya aikata kisan shima mai gaskiya ne idan ki kai la’akari da yanayi da furucin bakinsa zaki san ba da gangan ya aikata wannan laifiba” Ta fara yi mata lissafi tana nuna mata da hannu. “da farko kinga lauyar da zamu yi shari’ar da shi Barrister Haidar Aliyu, kowa ya san wane ne shi a zahirance, ga alkalin da zai yanke hukuncin shari’ar Justice Musaddiq, dan sandan da ya yi bincike a kan case din ASP Mubarak, likitan da ya dubata ya tabbatar ta mutu Doctor Kabeer” 20(ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA DAYA, NA NURA S GARO) Barrister Zahra ta yi shiru tana girgiza kai fuskarta bayyane da alamun damuwa ta ci gaba da cewa, “zan iya rantse miki duk cikin wadannan mutanen da na lissafo bawanda zai iya kar6ar koda naira biyar ne domin ya 6oye gaskiya, sannan kowa kwararre ne wajen aikinsa ballantana na ce an samu kuskure a cikin ayyukansu” Barrister Halima ta gyada kai domin gaskata abunda kawartata ta ke fadamata sannan ta ce, “na lura da haka wallahi tun ina jin tsoro harma na daina jin tsoro domin ke da kanki da ki ke kare hakkin wanda ya aikata laifin kema mai gaskiyace abun dai da na yarda da shi shi ne gaskiya da gaskiya ce za ta kara a wannan lokacin sai dai muyi fatan Allah ya nuna mana gaskiya ya bamu ikon binta” “ameen” Barrister Zahra ta amsa mata a lokacin da Barrister Halima ta tsaya a bakin kofar gidansu Zahra ta danna hon domin mai gadi ya bude musu gate su shiga. Da sauri kuwa ya bude yana mai gaggawa Halima ta kalleshi a kokarinta na shiga gidan ta ce mishi, “dan tsaya karka kulle mai gadi yanzu zan fita” “to Hajiya” Mai gadin ya amsa mata cikin girmamawa. Barrister Zahra ta kalleta ta ce, “bazaki bari mu shiga cikin gida mu ci abinci ba sai ki tafi?” Barrister Halima ta girgiza mata kai hade da cewa, “gaskiya lokaci ya kure Barrister ya kamata na je gida na yi abunda ya kamata kinga dai bamu da lokaci gashi gobe karfe goma na safe za mu shiga kotu” “haka ne” Barrister Zahra ta ce, a lokacin ne Barrister Halima ta samu waje ta yi parking din motar, ta cire mukullin ta mika wa Zahra sannan ta sa hannu a cikin jakarta ta dauko hotunan da suka kar6o a wajen ASP Ibrahim ta mika mata. “ga wadannan hotunan ko zaki yi wani amfanin da su” Barrister Zahra ta sa hannu ta kar6i hotunan da Halima ke miko mata sannan ta ce,

LITTAFIN ZAHIRIN KAUNA NA DAYA


ZAHIRIN KAUNA
Nura Isa S Garo

11(ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA DAYA, NA NURA S GARO) “wallahi Mama wata shari’a zamu shiga gobe kuma ban gama tattara bayanan da nake son samu ba shi ya sa na ce Barrister Halima ta biyomun yau da wuri mu fita kar lokaci ya kuremana” “Allah ya taimaka” Mahaifiyarta ta ce mata a takaice sannan ta mike daga zaunen da ta ke akan doguwar kujerar tana nuna mata dining inda abinci ke jere akai ta ci gaba da cewa, “sai muje ki ci abinci kyafi samun kuzarin gudanar da bincinken yadda ya kamata” “to Mama” Barrister Zahra ta amsa tana mai fadada murmushin kan fuskarta, ta mike daga tsugunnan da ta ke ta karasa kan dining table din ta samu kujerar kusa da Mahaifiyarta ta ja ta zauna sannan ta ja flask din shayi ta zuzzuba musu a kofuna kamar yadda suka saba. tsawon minti goma suka kwashe suna cin abincin bayan sun gama ne Zahra ta dauki wayarta tana kokarin kiran Halima ta jiyo sallamarta don haka ta mayar da wayar cikin jaka sannan ta saita kallonta zuwa bakin kofar shigowa gidan inda suka hada ido da Halima a kokarin da ta ke na shigowa da murmushin a kan fuskarta ta tsugunna har kasa ta gaishe da Mahaifiyar Zahra sannan ta tashi ta mikawa Zahra hannu sukai musabiha sunawa junansu murmushi, Zahra ta nuna mata kujera ta ce, “bismilla ki fara cin abinci sai mu tafi ko?” Barrister Halima ta girgiza kai tana murmushi ta ce, “kema kinsan bayadda za a yi Hajiya ta barni na fito daga gida batare da na karya ba, wallahi na koshi sosai cikinnan nawa ba masaka tsinke” “ya yi kyau!” Barrister Zahra ta ce lokacin da ta ke kokarin mikewa daga kan kujerar da ta ke zaune ta kalli Mahaifiyarta wacce ta zuba musu ido tana kallonsu cikin fara’a da sakin fuska. Ta ce, “to Mama zamu tafi” Justice Aisha ta kalleta tana murmushi ta ce, “Allah ya dawo da ku lafiya ya bada sa’a. haka nake son mutum da bada himma akan aikinsa. Har kun tunomun nima lokacin da nake ganiyar aikina na shari’a inhar ina da case a kotu hankalina baya kwanciya sai na ga na gama” Gaba daya sukai dariya ba tare da sunyi maganaba hakance ta sa Justice Aisha kara kallonsu a karo na biyu ta ce, 12(ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA DAYA, NA NURA S GARO) “sai kun dawo ‘ya’yannan amman don Allah ku yi kokari ku fitar da mazajen aure dan ba mayar da hankali akan aikin kawai nake son naga kunyiba ina son na ga kowacce ta kawomun mijin da za ta aura” Dariya suka karayi lokacin da suka juya suka fara tafiya da zummar fita daga cikin falon har sunkai bakin kofa Zahra ta waigo ta kalli Mahaifiyarta da guntun murmushinta ta ce, “ki kwantar da hankalinki Mamana ana gama wannan shari’ar insha Allah duk zamu gabato miki da surukanki ki tantancesu in sun cancanta ki basu in basu cancantaba mu kawo miki wasu” “Allah ya sa” Justice Aisha ta amsa cikin jin dadin amsar da ‘yarta ta bata domin a koda yaushe burinta bai wuce ta ga ‘yammatan biyu sun tsayar da mazajen aureba ganin tsayin lokacin da suka kwashe amman ba wacce ta ke zancen aure. Zahra da Halima sukai murmushi sannan suka fita daga cikin gidan suka karasa tsakiyar farfajiyar da motocin ke ajje suka shiga Motar Zahra ta jasu mai gadi ya bude musu gate suka fita. A hankula cikin nutsuwa Zahra ta ke jan motar lokacin da ta ke sauka daga cikin layinsu da ke kan titin President Avenue, Nassarawa G.R.A Kano ta juya sitiyarin motar suka hau tiin Hadejia Road. sun fara tafiya ne Halima ta kalli Zahra tana sassauta murmushin kan fuskata ta ce, “yanzu ta ina zamu fara?” Zahra ta waiga ta kalleta sannan ta mayar da hankalinta kan tukin da ta ke ta ce, “nan bampai zamu shiga kin san a nan suka ajjeshi sai gobe in an kaishi kotu dagacan za a zarce da shi sashin masu manyan laifika na bursin din kurmawa” “to Allah ya kiyaye” Halima ta ce, “ameen” Zahra ta amsa mata cikin nutsuwa tare da mayar da hankalinta kan tukin da ta ke lokacin da ta ke karya kwana domin hawa kan titin mission road. Tafiyar minti biyar ce ta kaisu sashen masu manyan laifuka na ofishin ‘yan sandan kasancewar babu nisa a tsakaninsu, Zahra ta samu waje ta yi parking a wajen da aka tanada domin ajje motoci sannan suka fito suna tafiya cikin nutsuwa suka jera domin shiga cikin ofishin ‘yan sandan. 13(ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA DAYA, NA NURA S GARO) Kai tsaye sashen masu kula da manyan laifi suka tunkara kasancewar ba wannan ba ne karon farko da suka fara shiga cikin ofishin kusanma ya zamar musu jiki domin duk wani babban laifi tanan suke fara bincikensa kafun su shiga kotu. Inspector Bashir suka tarar yana zaune a kan kujerarsa ya dunkufar da kai yana rubuce-rubuce, sallarmar da su Zahra suka yi ce ta sa ya dago da kansa da sauri da murmushi a kanfuskarsa ya amsa musu domin sun saba da shi sosai. “lallai yau muna da manyan baki, Barrister Zahra, Barrister Halima sannunku da zuwa” “yauwa sannunka da aiki Bashir” Barrister Zahra ta amsa mishi da murmushi a kan fuskarta lokacin da suke kokarin zama a kan kujerun da ke jere a gaban table din ofishinnasa. Da sauri Inspector Bashir ya mike yana cewa, “bari na kawo muku lemo” “a’a Inspector barshi kawai yanzu muka gama karyawa sannan muka fito mungode” Barrister Halima ce ta dakatar da shi don haka ya koma ya zauna tare da nutsuwa ya basu dukkan hankalinsa. Barrister Zahra ce ta yi gyaran murya lokacin da taga Inspector bashir ya nutsu yana sauraronsu sannan ta fara da cewa, “Bashir daman muna da wani case ne wanda za a shiga kotu gobe, shi ne muka biyo bayan wanda ake zargi domin yi mishi wasu tambayoyi” Inspector Bashir ya daga mata kai cikin girmamawa tare da janyo Computer da ke gabansa yana kallo ya ce, “haka ne Hajiya, ya sunan suspect din na duba muku?” “Alhaji Mukhtar Mai Gaskiya” da sauri Inspector Bashir ya kalli Barrister Zahra da alamun damuwa akan fuskarsa ya ce, “Hajiya anya kuwa kin san Barristan da zaki kara da shi a kotu kuwa?” Barrister Zahra ta kalli Inspector Bashir babu alamun faduwar gaba a kan fuskarta ta ce, “eh Barrister Haidar ko?” “eh shi ne” Inspector Bashir ya bata amsa har a lokacin da alamun damuwar a kan fuskarsa. Barrister Zahra da Halima sukai murmushi cikin nuna karfin gwiwa suka kalli juna sannan suka mayar da kallonsu kan Inspector Bashir, Barrister Zahra ta ce, 14(ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA DAYA, NA NURA S GARO) “na sani, ai shari’a ce Inspector ba da wanda bata hadawa. takan hada Uba da [ansa ko Miji da Matarsa don haka ba laifi ba ne dan Malami da [alibarsa sun goga a wannan karon” Inspector Bashir ya gyada mata kai ya ce, “haka ne Hajiya, nima ba wani abu na gujemiki ba sai record nasan dukkan wani lauya yana takama da irin nasarorin da ya yi a shari’arsa sannan yana kiyayewa domin kare darajarsa” Barrister Zahra ta ce, “haka maganarka ta ke, kamar yadda yanzunma Allah ne kadai ya san mai gaskiya da kuma wanda zai yi nasara” “to Allah ya bada sa’a” Bashir ya ce, sannan ya mayar da hankalinsa wajen shigar da sunan da ya ke a cikin computar bayan ya gama ne ya mike tsaye jikinsa ba kwari ya ce, “muje na kaiku inda ya ke” “to Bashir mungode” Suka ce mishi a tare lokacin da suke mikewa tsaye, Bashir ya shiga gaba suna biye da shi a baya har dakin da aka kulle Alhaji Mukhtar, wanda suka tarar da shi yana zaune ya dunkufar da kai tare da juyawa kofar dakin baya, ya yi shiru baya ko kwakwkwaran motsi. Inspector Bashir ya kallesu ya ce, “to Hajiya ni zan koma sai kun fito” “mun gode” Suka amsa mishi a tare Bashir ya juya ya tafi ya barsu a tsaye a bakin kofar dakin da Alhaji Mukhtar ke kulle inda suka zubawa dattijon mutumin ido suna kallonshi na dan wani lokaci ba tare da sun yi mishi maganaba. Sun kwashe tsawon minti biyu zuwa uku bawanda ya yi magana sannan Barrister Zahra ta yi gyaran murya tare da yi mishi sallama. “assalamu alaika” “ameen wa’alaikumussalam” Tattausar muryar dattijon ta daki dodan kunnensu, wanda ke magana cikin nutsuwa da kamala tamkar ba shi ake zargi da hukuncin kisan kai ba. Barrister Zahra ce ta ci gaba da magana da cewa, “sunana Barrister Zahra Muhammad, wannan kuma abokiyar aikina ce Barrister Halima Mahmoud. Mu ne lauyoyin da zamu kareka a shari’ar da za a gudanar gobe in Allah ya kaimu shi ne muka zo domin mu yi maka wasu tambayoyi da muke fatan zaka bamu hadin kai domin mu gudanar da aikinmu cikin nasara” 15(ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA DAYA, NA NURA S GARO) Barrister Zahra ta kai karshen maganar da ta ke amman tamkar tana fadawa dutse domin dattijon mutumin ko kwakwkwaran motsi bai yi ba tun daga amsa sallamar da ya yi ballantana ya waigo ya kulasu kamar yadda suka bukataba. “danka Umar Mukhtar shi ya daukemu a matsayin lauyoyin da zamu kareka” Ambaton sunan ‘danka Umar Mukhtar’ da Barrister Zahra ta yi ne ya sa a hankali dattijon mutumin ya waigo cikin nutsuwa ya kallesu da tattausan murmushi a kan fuskarsa, suka bishi da kallo a tare. Fari ne, yana da doguwar fuska mai cike da farar kasumba. Kallo daya zaka yi mishi ka fahimci akwai nutsuwa da jin dadi a tattare da shi, ga wani tattausan murmushi bayyane a kan fuskarsa wanda suka kasa gane murmushin me ya ke. ya dauki wasu ‘yan dakiku yana kare musu kallo yayinda murmushin kan fuskarsa ke kara fadada sannan ya taso tsam daga inda ya ke zaune, ya karasa bakin kofar ya dafa karfen da ya yi mishi iyaka da su Barrister Zahra. “barkanku da zuwa” Alhaji Mukhtar ya katse musu tunanin da suke ta hanyar yi musu magana sannan ya zuba musu ido yana kallonsu. “barka dai Baba” Barrister Halima ta yi karfin halin amsa mishi sannan ta sa hannu ta ta6a Barrister Zahra ganin ta kurawa dattijon mutumin ido tana kallonshi cikin mamaki bata ko kiftawa. Ganin Barrister Zahra ta dan nutsu ne ya sa Halima ta mayar da kallonta kan dattijon mutumin cikin tausasa murya domin ba shi girmansa ta fara yi mishi magana da cewa, “Baba wasu tambayoyi muke son yi maka, muna fatan zaka bamu hadin kai ka fadamana gaskiyar abunda ka sani” Alhaji Mukhtar ya fadada murmushin kan fuskarsa ya ce, “insha Allahu ‘yata, zan baku cikakken bayani duk da nasan [ana bai turoku wajena domin ku yi nasara ba, ya turomun ku ne kawai domin ya nunamun soyayya da kulawa” Mamakin Barrister Zahra ya kara munana jin bayanin da ke fita daga cikin bakin Alhaji Mukhtar, lokaci daya duk ta dabarbarce ta kasa yimai tambayar da ta ke son yi mishi. Barrister Halima ce ta kara yin ta maza a karo na biyu ta ce,11(ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA DAYA, NA NURA S GARO) “wallahi Mama wata shari’a zamu shiga gobe kuma ban gama tattara bayanan da nake son samu ba shi ya sa na ce Barrister Halima ta biyomun yau da wuri mu fita kar lokaci ya kuremana” “Allah ya taimaka” Mahaifiyarta ta ce mata a takaice sannan ta mike daga zaunen da ta ke akan doguwar kujerar tana nuna mata dining inda abinci ke jere akai ta ci gaba da cewa, “sai muje ki ci abinci kyafi samun kuzarin gudanar da bincinken yadda ya kamata” “to Mama” Barrister Zahra ta amsa tana mai fadada murmushin kan fuskarta, ta mike daga tsugunnan da ta ke ta karasa kan dining table din ta samu kujerar kusa da Mahaifiyarta ta ja ta zauna sannan ta ja flask din shayi ta zuzzuba musu a kofuna kamar yadda suka saba. tsawon minti goma suka kwashe suna cin abincin bayan sun gama ne Zahra ta dauki wayarta tana kokarin kiran Halima ta jiyo sallamarta don haka ta mayar da wayar cikin jaka sannan ta saita kallonta zuwa bakin kofar shigowa gidan inda suka hada ido da Halima a kokarin da ta ke na shigowa da murmushin a kan fuskarta ta tsugunna har kasa ta gaishe da Mahaifiyar Zahra sannan ta tashi ta mikawa Zahra hannu sukai musabiha sunawa junansu murmushi, Zahra ta nuna mata kujera ta ce, “bismilla ki fara cin abinci sai mu tafi ko?” Barrister Halima ta girgiza kai tana murmushi ta ce, “kema kinsan bayadda za a yi Hajiya ta barni na fito daga gida batare da na karya ba, wallahi na koshi sosai cikinnan nawa ba masaka tsinke” “ya yi kyau!” Barrister Zahra ta ce lokacin da ta ke kokarin mikewa daga kan kujerar da ta ke zaune ta kalli Mahaifiyarta wacce ta zuba musu ido tana kallonsu cikin fara’a da sakin fuska. Ta ce, “to Mama zamu tafi” Justice Aisha ta kalleta tana murmushi ta ce, “Allah ya dawo da ku lafiya ya bada sa’a. haka nake son mutum da bada himma akan aikinsa. Har kun tunomun nima lokacin da nake ganiyar aikina na shari’a inhar ina da case a kotu hankalina baya kwanciya sai na ga na gama” Gaba daya sukai dariya ba tare da sunyi maganaba hakance ta sa Justice Aisha kara kallonsu a karo na biyu ta ce, 12(ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA DAYA, NA NURA S GARO) “sai kun dawo ‘ya’yannan amman don Allah ku yi kokari ku fitar da mazajen aure dan ba mayar da hankali akan aikin kawai nake son naga kunyiba ina son na ga kowacce ta kawomun mijin da za ta aura” Dariya suka karayi lokacin da suka juya suka fara tafiya da zummar fita daga cikin falon har sunkai bakin kofa Zahra ta waigo ta kalli Mahaifiyarta da guntun murmushinta ta ce, “ki kwantar da hankalinki Mamana ana gama wannan shari’ar insha Allah duk zamu gabato miki da surukanki ki tantancesu in sun cancanta ki basu in basu cancantaba mu kawo miki wasu” “Allah ya sa” Justice Aisha ta amsa cikin jin dadin amsar da ‘yarta ta bata domin a koda yaushe burinta bai wuce ta ga ‘yammatan biyu sun tsayar da mazajen aureba ganin tsayin lokacin da suka kwashe amman ba wacce ta ke zancen aure. Zahra da Halima sukai murmushi sannan suka fita daga cikin gidan suka karasa tsakiyar farfajiyar da motocin ke ajje suka shiga Motar Zahra ta jasu mai gadi ya bude musu gate suka fita. A hankula cikin nutsuwa Zahra ta ke jan motar lokacin da ta ke sauka daga cikin layinsu da ke kan titin President Avenue, Nassarawa G.R.A Kano ta juya sitiyarin motar suka hau tiin Hadejia Road. sun fara tafiya ne Halima ta kalli Zahra tana sassauta murmushin kan fuskata ta ce, “yanzu ta ina zamu fara?” Zahra ta waiga ta kalleta sannan ta mayar da hankalinta kan tukin da ta ke ta ce, “nan bampai zamu shiga kin san a nan suka ajjeshi sai gobe in an kaishi kotu dagacan za a zarce da shi sashin masu manyan laifika na bursin din kurmawa” “to Allah ya kiyaye” Halima ta ce, “ameen” Zahra ta amsa mata cikin nutsuwa tare da mayar da hankalinta kan tukin da ta ke lokacin da ta ke karya kwana domin hawa kan titin mission road. Tafiyar minti biyar ce ta kaisu sashen masu manyan laifuka na ofishin ‘yan sandan kasancewar babu nisa a tsakaninsu, Zahra ta samu waje ta yi parking a wajen da aka tanada domin ajje motoci sannan suka fito suna tafiya cikin nutsuwa suka jera domin shiga cikin ofishin ‘yan sandan. 13(ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA DAYA, NA NURA S GARO) Kai tsaye sashen masu kula da manyan laifi suka tunkara kasancewar ba wannan ba ne karon farko da suka fara shiga cikin ofishin kusanma ya zamar musu jiki domin duk wani babban laifi tanan suke fara bincikensa kafun su shiga kotu. Inspector Bashir suka tarar yana zaune a kan kujerarsa ya dunkufar da kai yana rubuce-rubuce, sallarmar da su Zahra suka yi ce ta sa ya dago da kansa da sauri da murmushi a kanfuskarsa ya amsa musu domin sun saba da shi sosai. “lallai yau muna da manyan baki, Barrister Zahra, Barrister Halima sannunku da zuwa” “yauwa sannunka da aiki Bashir” Barrister Zahra ta amsa mishi da murmushi a kan fuskarta lokacin da suke kokarin zama a kan kujerun da ke jere a gaban table din ofishinnasa. Da sauri Inspector Bashir ya mike yana cewa, “bari na kawo muku lemo” “a’a Inspector barshi kawai yanzu muka gama karyawa sannan muka fito mungode” Barrister Halima ce ta dakatar da shi don haka ya koma ya zauna tare da nutsuwa ya basu dukkan hankalinsa. Barrister Zahra ce ta yi gyaran murya lokacin da taga Inspector bashir ya nutsu yana sauraronsu sannan ta fara da cewa, “Bashir daman muna da wani case ne wanda za a shiga kotu gobe, shi ne muka biyo bayan wanda ake zargi domin yi mishi wasu tambayoyi” Inspector Bashir ya daga mata kai cikin girmamawa tare da janyo Computer da ke gabansa yana kallo ya ce, “haka ne Hajiya, ya sunan suspect din na duba muku?” “Alhaji Mukhtar Mai Gaskiya” da sauri Inspector Bashir ya kalli Barrister Zahra da alamun damuwa akan fuskarsa ya ce, “Hajiya anya kuwa kin san Barristan da zaki kara da shi a kotu kuwa?” Barrister Zahra ta kalli Inspector Bashir babu alamun faduwar gaba a kan fuskarta ta ce, “eh Barrister Haidar ko?” “eh shi ne” Inspector Bashir ya bata amsa har a lokacin da alamun damuwar a kan fuskarsa. Barrister Zahra da Halima sukai murmushi cikin nuna karfin gwiwa suka kalli juna sannan suka mayar da kallonsu kan Inspector Bashir, Barrister Zahra ta ce, 14(ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA DAYA, NA NURA S GARO) “na sani, ai shari’a ce Inspector ba da wanda bata hadawa. takan hada Uba da [ansa ko Miji da Matarsa don haka ba laifi ba ne dan Malami da [alibarsa sun goga a wannan karon” Inspector Bashir ya gyada mata kai ya ce, “haka ne Hajiya, nima ba wani abu na gujemiki ba sai record nasan dukkan wani lauya yana takama da irin nasarorin da ya yi a shari’arsa sannan yana kiyayewa domin kare darajarsa” Barrister Zahra ta ce, “haka maganarka ta ke, kamar yadda yanzunma Allah ne kadai ya san mai gaskiya da kuma wanda zai yi nasara” “to Allah ya bada sa’a” Bashir ya ce, sannan ya mayar da hankalinsa wajen shigar da sunan da ya ke a cikin computar bayan ya gama ne ya mike tsaye jikinsa ba kwari ya ce, “muje na kaiku inda ya ke” “to Bashir mungode” Suka ce mishi a tare lokacin da suke mikewa tsaye, Bashir ya shiga gaba suna biye da shi a baya har dakin da aka kulle Alhaji Mukhtar, wanda suka tarar da shi yana zaune ya dunkufar da kai tare da juyawa kofar dakin baya, ya yi shiru baya ko kwakwkwaran motsi. Inspector Bashir ya kallesu ya ce, “to Hajiya ni zan koma sai kun fito” “mun gode” Suka amsa mishi a tare Bashir ya juya ya tafi ya barsu a tsaye a bakin kofar dakin da Alhaji Mukhtar ke kulle inda suka zubawa dattijon mutumin ido suna kallonshi na dan wani lokaci ba tare da sun yi mishi maganaba. Sun kwashe tsawon minti biyu zuwa uku bawanda ya yi magana sannan Barrister Zahra ta yi gyaran murya tare da yi mishi sallama. “assalamu alaika” “ameen wa’alaikumussalam” Tattausar muryar dattijon ta daki dodan kunnensu, wanda ke magana cikin nutsuwa da kamala tamkar ba shi ake zargi da hukuncin kisan kai ba. Barrister Zahra ce ta ci gaba da magana da cewa, “sunana Barrister Zahra Muhammad, wannan kuma abokiyar aikina ce Barrister Halima Mahmoud. Mu ne lauyoyin da zamu kareka a shari’ar da za a gudanar gobe in Allah ya kaimu shi ne muka zo domin mu yi maka wasu tambayoyi da muke fatan zaka bamu hadin kai domin mu gudanar da aikinmu cikin nasara” 15(ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA DAYA, NA NURA S GARO) Barrister Zahra ta kai karshen maganar da ta ke amman tamkar tana fadawa dutse domin dattijon mutumin ko kwakwkwaran motsi bai yi ba tun daga amsa sallamar da ya yi ballantana ya waigo ya kulasu kamar yadda suka bukataba. “danka Umar Mukhtar shi ya daukemu a matsayin lauyoyin da zamu kareka” Ambaton sunan ‘danka Umar Mukhtar’ da Barrister Zahra ta yi ne ya sa a hankali dattijon mutumin ya waigo cikin nutsuwa ya kallesu da tattausan murmushi a kan fuskarsa, suka bishi da kallo a tare. Fari ne, yana da doguwar fuska mai cike da farar kasumba. Kallo daya zaka yi mishi ka fahimci akwai nutsuwa da jin dadi a tattare da shi, ga wani tattausan murmushi bayyane a kan fuskarsa wanda suka kasa gane murmushin me ya ke. ya dauki wasu ‘yan dakiku yana kare musu kallo yayinda murmushin kan fuskarsa ke kara fadada sannan ya taso tsam daga inda ya ke zaune, ya karasa bakin kofar ya dafa karfen da ya yi mishi iyaka da su Barrister Zahra. “barkanku da zuwa” Alhaji Mukhtar ya katse musu tunanin da suke ta hanyar yi musu magana sannan ya zuba musu ido yana kallonsu. “barka dai Baba” Barrister Halima ta yi karfin halin amsa mishi sannan ta sa hannu ta ta6a Barrister Zahra ganin ta kurawa dattijon mutumin ido tana kallonshi cikin mamaki bata ko kiftawa. Ganin Barrister Zahra ta dan nutsu ne ya sa Halima ta mayar da kallonta kan dattijon mutumin cikin tausasa murya domin ba shi girmansa ta fara yi mishi magana da cewa, “Baba wasu tambayoyi muke son yi maka, muna fatan zaka bamu hadin kai ka fadamana gaskiyar abunda ka sani” Alhaji Mukhtar ya fadada murmushin kan fuskarsa ya ce, “insha Allahu ‘yata, zan baku cikakken bayani duk da nasan [ana bai turoku wajena domin ku yi nasara ba, ya turomun ku ne kawai domin ya nunamun soyayya da kulawa” Mamakin Barrister Zahra ya kara munana jin bayanin da ke fita daga cikin bakin Alhaji Mukhtar, lokaci daya duk ta dabarbarce ta kasa yimai tambayar da ta ke son yi mishi. Barrister Halima ce ta kara yin ta maza a karo na biyu ta ce,11(ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA DAYA, NA NURA S GARO) “wallahi Mama wata shari’a zamu shiga gobe kuma ban gama tattara bayanan da nake son samu ba shi ya sa na ce Barrister Halima ta biyomun yau da wuri mu fita kar lokaci ya kuremana” “Allah ya taimaka” Mahaifiyarta ta ce mata a takaice sannan ta mike daga zaunen da ta ke akan doguwar kujerar tana nuna mata dining inda abinci ke jere akai ta ci gaba da cewa, “sai muje ki ci abinci kyafi samun kuzarin gudanar da bincinken yadda ya kamata” “to Mama” Barrister Zahra ta amsa tana mai fadada murmushin kan fuskarta, ta mike daga tsugunnan da ta ke ta karasa kan dining table din ta samu kujerar kusa da Mahaifiyarta ta ja ta zauna sannan ta ja flask din shayi ta zuzzuba musu a kofuna kamar yadda suka saba. tsawon minti goma suka kwashe suna cin abincin bayan sun gama ne Zahra ta dauki wayarta tana kokarin kiran Halima ta jiyo sallamarta don haka ta mayar da wayar cikin jaka sannan ta saita kallonta zuwa bakin kofar shigowa gidan inda suka hada ido da Halima a kokarin da ta ke na shigowa da murmushin a kan fuskarta ta tsugunna har kasa ta gaishe da Mahaifiyar Zahra sannan ta tashi ta mikawa Zahra hannu sukai musabiha sunawa junansu murmushi, Zahra ta nuna mata kujera ta ce, “bismilla ki fara cin abinci sai mu tafi ko?” Barrister Halima ta girgiza kai tana murmushi ta ce, “kema kinsan bayadda za a yi Hajiya ta barni na fito daga gida batare da na karya ba, wallahi na koshi sosai cikinnan nawa ba masaka tsinke” “ya yi kyau!” Barrister Zahra ta ce lokacin da ta ke kokarin mikewa daga kan kujerar da ta ke zaune ta kalli Mahaifiyarta wacce ta zuba musu ido tana kallonsu cikin fara’a da sakin fuska. Ta ce, “to Mama zamu tafi” Justice Aisha ta kalleta tana murmushi ta ce, “Allah ya dawo da ku lafiya ya bada sa’a. haka nake son mutum da bada himma akan aikinsa. Har kun tunomun nima lokacin da nake ganiyar aikina na shari’a inhar ina da case a kotu hankalina baya kwanciya sai na ga na gama” Gaba daya sukai dariya ba tare da sunyi maganaba hakance ta sa Justice Aisha kara kallonsu a karo na biyu ta ce, 12(ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA DAYA, NA NURA S GARO) “sai kun dawo ‘ya’yannan amman don Allah ku yi kokari ku fitar da mazajen aure dan ba mayar da hankali akan aikin kawai nake son naga kunyiba ina son na ga kowacce ta kawomun mijin da za ta aura” Dariya suka karayi lokacin da suka juya suka fara tafiya da zummar fita daga cikin falon har sunkai bakin kofa Zahra ta waigo ta kalli Mahaifiyarta da guntun murmushinta ta ce, “ki kwantar da hankalinki Mamana ana gama wannan shari’ar insha Allah duk zamu gabato miki da surukanki ki tantancesu in sun cancanta ki basu in basu cancantaba mu kawo miki wasu” “Allah ya sa” Justice Aisha ta amsa cikin jin dadin amsar da ‘yarta ta bata domin a koda yaushe burinta bai wuce ta ga ‘yammatan biyu sun tsayar da mazajen aureba ganin tsayin lokacin da suka kwashe amman ba wacce ta ke zancen aure. Zahra da Halima sukai murmushi sannan suka fita daga cikin gidan suka karasa tsakiyar farfajiyar da motocin ke ajje suka shiga Motar Zahra ta jasu mai gadi ya bude musu gate suka fita. A hankula cikin nutsuwa Zahra ta ke jan motar lokacin da ta ke sauka daga cikin layinsu da ke kan titin President Avenue, Nassarawa G.R.A Kano ta juya sitiyarin motar suka hau tiin Hadejia Road. sun fara tafiya ne Halima ta kalli Zahra tana sassauta murmushin kan fuskata ta ce, “yanzu ta ina zamu fara?” Zahra ta waiga ta kalleta sannan ta mayar da hankalinta kan tukin da ta ke ta ce, “nan bampai zamu shiga kin san a nan suka ajjeshi sai gobe in an kaishi kotu dagacan za a zarce da shi sashin masu manyan laifika na bursin din kurmawa” “to Allah ya kiyaye” Halima ta ce, “ameen” Zahra ta amsa mata cikin nutsuwa tare da mayar da hankalinta kan tukin da ta ke lokacin da ta ke karya kwana domin hawa kan titin mission road. Tafiyar minti biyar ce ta kaisu sashen masu manyan laifuka na ofishin ‘yan sandan kasancewar babu nisa a tsakaninsu, Zahra ta samu waje ta yi parking a wajen da aka tanada domin ajje motoci sannan suka fito suna tafiya cikin nutsuwa suka jera domin shiga cikin ofishin ‘yan sandan. 13(ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA DAYA, NA NURA S GARO) Kai tsaye sashen masu kula da manyan laifi suka tunkara kasancewar ba wannan ba ne karon farko da suka fara shiga cikin ofishin kusanma ya zamar musu jiki domin duk wani babban laifi tanan suke fara bincikensa kafun su shiga kotu. Inspector Bashir suka tarar yana zaune a kan kujerarsa ya dunkufar da kai yana rubuce-rubuce, sallarmar da su Zahra suka yi ce ta sa ya dago da kansa da sauri da murmushi a kanfuskarsa ya amsa musu domin sun saba da shi sosai. “lallai yau muna da manyan baki, Barrister Zahra, Barrister Halima sannunku da zuwa” “yauwa sannunka da aiki Bashir” Barrister Zahra ta amsa mishi da murmushi a kan fuskarta lokacin da suke kokarin zama a kan kujerun da ke jere a gaban table din ofishinnasa. Da sauri Inspector Bashir ya mike yana cewa, “bari na kawo muku lemo” “a’a Inspector barshi kawai yanzu muka gama karyawa sannan muka fito mungode” Barrister Halima ce ta dakatar da shi don haka ya koma ya zauna tare da nutsuwa ya basu dukkan hankalinsa. Barrister Zahra ce ta yi gyaran murya lokacin da taga Inspector bashir ya nutsu yana sauraronsu sannan ta fara da cewa, “Bashir daman muna da wani case ne wanda za a shiga kotu gobe, shi ne muka biyo bayan wanda ake zargi domin yi mishi wasu tambayoyi” Inspector Bashir ya daga mata kai cikin girmamawa tare da janyo Computer da ke gabansa yana kallo ya ce, “haka ne Hajiya, ya sunan suspect din na duba muku?” “Alhaji Mukhtar Mai Gaskiya” da sauri Inspector Bashir ya kalli Barrister Zahra da alamun damuwa akan fuskarsa ya ce, “Hajiya anya kuwa kin san Barristan da zaki kara da shi a kotu kuwa?” Barrister Zahra ta kalli Inspector Bashir babu alamun faduwar gaba a kan fuskarta ta ce, “eh Barrister Haidar ko?” “eh shi ne” Inspector Bashir ya bata amsa har a lokacin da alamun damuwar a kan fuskarsa. Barrister Zahra da Halima sukai murmushi cikin nuna karfin gwiwa suka kalli juna sannan suka mayar da kallonsu kan Inspector Bashir, Barrister Zahra ta ce, 14(ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA DAYA, NA NURA S GARO) “na sani, ai shari’a ce Inspector ba da wanda bata hadawa. takan hada Uba da [ansa ko Miji da Matarsa don haka ba laifi ba ne dan Malami da [alibarsa sun goga a wannan karon” Inspector Bashir ya gyada mata kai ya ce, “haka ne Hajiya, nima ba wani abu na gujemiki ba sai record nasan dukkan wani lauya yana takama da irin nasarorin da ya yi a shari’arsa sannan yana kiyayewa domin kare darajarsa” Barrister Zahra ta ce, “haka maganarka ta ke, kamar yadda yanzunma Allah ne kadai ya san mai gaskiya da kuma wanda zai yi nasara” “to Allah ya bada sa’a” Bashir ya ce, sannan ya mayar da hankalinsa wajen shigar da sunan da ya ke a cikin computar bayan ya gama ne ya mike tsaye jikinsa ba kwari ya ce, “muje na kaiku inda ya ke” “to Bashir mungode” Suka ce mishi a tare lokacin da suke mikewa tsaye, Bashir ya shiga gaba suna biye da shi a baya har dakin da aka kulle Alhaji Mukhtar, wanda suka tarar da shi yana zaune ya dunkufar da kai tare da juyawa kofar dakin baya, ya yi shiru baya ko kwakwkwaran motsi. Inspector Bashir ya kallesu ya ce, “to Hajiya ni zan koma sai kun fito” “mun gode” Suka amsa mishi a tare Bashir ya juya ya tafi ya barsu a tsaye a bakin kofar dakin da Alhaji Mukhtar ke kulle inda suka zubawa dattijon mutumin ido suna kallonshi na dan wani lokaci ba tare da sun yi mishi maganaba. Sun kwashe tsawon minti biyu zuwa uku bawanda ya yi magana sannan Barrister Zahra ta yi gyaran murya tare da yi mishi sallama. “assalamu alaika” “ameen wa’alaikumussalam” Tattausar muryar dattijon ta daki dodan kunnensu, wanda ke magana cikin nutsuwa da kamala tamkar ba shi ake zargi da hukuncin kisan kai ba. Barrister Zahra ce ta ci gaba da magana da cewa, “sunana Barrister Zahra Muhammad, wannan kuma abokiyar aikina ce Barrister Halima Mahmoud. Mu ne lauyoyin da zamu kareka a shari’ar da za a gudanar gobe in Allah ya kaimu shi ne muka zo domin mu yi maka wasu tambayoyi da muke fatan zaka bamu hadin kai domin mu gudanar da aikinmu cikin nasara” 15(ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA DAYA, NA NURA S GARO) Barrister Zahra ta kai karshen maganar da ta ke amman tamkar tana fadawa dutse domin dattijon mutumin ko kwakwkwaran motsi bai yi ba tun daga amsa sallamar da ya yi ballantana ya waigo ya kulasu kamar yadda suka bukataba. “danka Umar Mukhtar shi ya daukemu a matsayin lauyoyin da zamu kareka” Ambaton sunan ‘danka Umar Mukhtar’ da Barrister Zahra ta yi ne ya sa a hankali dattijon mutumin ya waigo cikin nutsuwa ya kallesu da tattausan murmushi a kan fuskarsa, suka bishi da kallo a tare. Fari ne, yana da doguwar fuska mai cike da farar kasumba. Kallo daya zaka yi mishi ka fahimci akwai nutsuwa da jin dadi a tattare da shi, ga wani tattausan murmushi bayyane a kan fuskarsa wanda suka kasa gane murmushin me ya ke. ya dauki wasu ‘yan dakiku yana kare musu kallo yayinda murmushin kan fuskarsa ke kara fadada sannan ya taso tsam daga inda ya ke zaune, ya karasa bakin kofar ya dafa karfen da ya yi mishi iyaka da su Barrister Zahra. “barkanku da zuwa” Alhaji Mukhtar ya katse musu tunanin da suke ta hanyar yi musu magana sannan ya zuba musu ido yana kallonsu. “barka dai Baba” Barrister Halima ta yi karfin halin amsa mishi sannan ta sa hannu ta ta6a Barrister Zahra ganin ta kurawa dattijon mutumin ido tana kallonshi cikin mamaki bata ko kiftawa. Ganin Barrister Zahra ta dan nutsu ne ya sa Halima ta mayar da kallonta kan dattijon mutumin cikin tausasa murya domin ba shi girmansa ta fara yi mishi magana da cewa, “Baba wasu tambayoyi muke son yi maka, muna fatan zaka bamu hadin kai ka fadamana gaskiyar abunda ka sani” Alhaji Mukhtar ya fadada murmushin kan fuskarsa ya ce, “insha Allahu ‘yata, zan baku cikakken bayani duk da nasan [ana bai turoku wajena domin ku yi nasara ba, ya turomun ku ne kawai domin ya nunamun soyayya da kulawa” Mamakin Barrister Zahra ya kara munana jin bayanin da ke fita daga cikin bakin Alhaji Mukhtar, lokaci daya duk ta dabarbarce ta kasa yimai tambayar da ta ke son yi mishi. Barrister Halima ce ta kara yin ta maza a karo na biyu ta ce,

Monday, September 5, 2016

ZAHIRIN KAUNA

ZAHIRIN KAUNA
Nura Isah S. Garo
1(ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA DAYA, NA NURA S GARO)Kallo daya zaka yi wa fuskarta kasan akwai matsananciyar damuwa a tare da ita. Barrister Fatima Zahra Muhamma kenan, daya daga cikin gogaggu kuma kwararrun Lauyoyin da ake ji da su a nan gida Nigeria da ma sauran kasashen da ke makwabtaka damu sannan kuma ‘ya guda daya ga marigayi tsohon shugaban ‘yan sandan kasarnan. Fara ce mai matsakaicin tsayi, tana da dogwan hanci da ‘yar faffadar fuska tare da yalwar gashin kai wanda ta yi parkingdinshi ta kwantar da shi zuwa gadon bayanta. Tayi wata bayyananniyar ajiyar zuciya lokacin da ta karasa gaban tafkeken hotan Mahaifinta da kekafe a bangon da ke arewacin falon ta kura mishi ido tana kallonshi na dan wani lokaci. A zaune ya ke a cikin ofishinsa kasancewar lokacin da a ka dauki hotan yana tsaka da aikinsa a matsayinsa na shugaban ‘yan sandan kasar Nigeria.da murmushi bayyane a kan fuskarsa wanda hakan ke da nasaba da irin nasarorin da ya samu. “ki kasance mai gaskiya da rikon amana Fatima, wadannan ne makaman da na rike har na kawo matsayin da nake na shugabancin rundunar ‘yansandan kasarnan, na tabbata in zaki yi riko da wadannan abubuwa biyu zaki samu nasarorin da baki ta6a tsammaniba a rayuwarki” Barrister Zahra ta yi ajiyar zuciya lokacin da ta ke tuno irin nasihar da akoda yaushe Mahaifinta ya ke yawan yi mata a kan ta kasance mai gaskiya da rikon amana domin samun nasara a cikin rayuwarta, amman ya za ta yi da wannan sarkakkiyar shari’ar da ta tunkarota? Wannan ce tambayar da ta wuni tana yiwa kanta tun wayewar garin ranar lokacin da wani saurayi ya kirata a waya yake rokonta a kan ta taimakeshi ta ceto rayuwar Mahaifinsa wanda ke tsare a sashen masu manyan laifuka na ofishin ‘yan sanda ana tuhumarsa da laifin aikata kisan kai. Ta kara yin wata sassanyar ajiyar zuciya a karo na biyusannan ta juya ta jingina bayanta a jikin bangon falon saitin inda hotan Mahaifinnata ya ke ta daga kanta sama tare da dulmiyawa cikin duniyar tunani. Shekararta dai-dai har bakwai tana aikin shari’a amman bata ta6a gamuwa da sarkakkiyar shari’a irin wannan ba, bata ta6a haduwa da tashin hankali kwatan kwacin wannanba. Me ya ke shirn faruwa da ita ne? 2(ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA DAYA, NA NURA S GARO) Sallamar da ta ji anayi ce ta katse mata tunanin da ta ke, ta mayar da kallonta bakin kofar tare da amsa sallamar domin bawa wanda zai shigo izinin shigowa. “amin wa’alaiki assalam, Barrister, bismillah shigo” Barrister Zahra ta amsa sallamar tare da bayar da izinin shigowa ga mai yin sallamar lokacin da ta fuskanci kawarta, aminiyarta, kuma abokiyar aikinta Barrister Halimatussa’adiyya Mahmoud ce ta ke yin sallamar wacce a dabi’unta ba ta shiga daki ko falon mutum har sai ya bata izini domin yin koyi da biyayya ga umarnin fiyayyen halitta Manzon Allah Annabi Muhammad (S.A.W). Barrister Halima ta shigo tana tafiya a hankula cikin nutsuwa tare da tauna cingum din da ke bakinta cikin gwaninta, fuskarta sanye da farin tabarau wanda aka kera jikinsa da narkakkiyar azurfa mai daukar ido.Ba sai ka tambaya ba kallo daya zaka yi mata kasan ta amsa sunanta na zama daya daga cikin manya manya kuma gogaggun lauyoyin kasar Nigeria.wata koriyar atamfa dinkin doguwar riga ce a jikinta wacce akai mata ratsin ado da wasu fararen duwatsu tun daga saman wuyan rigar har zuwa kasanta. fuskarta dauke da murmushi wanda baka rasata da shi a ko da yaushe kasancewarta mace mai yawan fara’a da barkwanci, ga iya tsara magana da fitar da lafazin bakinta yadda mai sauraronta zai gamsu da duk bayanan da ke fita daga bakinta. Ganin alamun damuwar da ke bayyane a kan fuskar Barrister Zahra ne ya sa Barrister Halima ta sassauta murmushin kan fuskarta a yayin da ta kekarasawa gaban aminiyartata ta dafa kafadarta da alamun mamaki bayyane akan fuskarta ta ce, “lafiya Zahra, Meke damunki na ga kin shiga cikin damuwa da firgici haka wanda tunda nake a rayuwata ban ta6a ganinki a cikin kwatan kwacin irinsa ba?” Barrister Zahra ta yi ajiyar zuciya tare da nunawa Halima kujerun da ke jere reras sun yiwa falon kawanya ta ce, “doguwar magana ce Barrister yakamata mu samu waje mu zauna domin halinnan da kika ganni a ciki wunin ranar yau haka na yi shi a karshe na yanke shawarar kiranki domin ance hannu biyu maganin kazamar miya, kuma abokin kuka shi ake fadawa mutuwa” 3(ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA DAYA, NA NURA S GARO)Da sauri Barrister Halima ta samu kujera ta zauna yayinda lokacidaya murmushin da ya rage a kan fuskarta ya yaye, matsananciyar damuwa ta samu gurbin zama a kan fuskarta domin ta san duk abunda da ya jefa kawarta cikin wannan hali na damuwa to ba karamun abu ba ne. Barrister Zahra ta samu karamar kujerar da ke ajje a gefen wacce Barrister Halima ke zauneitama ta zauna suka fuskanci juna sannan ta fara yi mata bayani cikin nutsuwa tayadda kawartata za ta fuskanci abunda ta ke fada. “wata sarkakkiyar shari’a ce ta tunkaromu Halima” Barrister Zahra ta ce da kawartata lokacin da ta ga ta gama kaguwa domin jin abunda ta ke son sanar da ita. “wacce irin shari’a ce wannan Zahra?” Halima ta tambayeta cikin gaggawa da alamun mamaki karara a kan fuskarta. “shari’ar kisa!” Barrister Zahra ta bata amsa, ganin Halima ta yi shiru tana kallonta ne ya sa ta ci gaba da cewa, “da misalin karfe goma na safiyar yau ne wani saurayi ya kirani yana kuka tamkar ransa zai fita yana rokona akan na taimaka na zamo lauyar da za ta kare Mahaifinshi” Barrister Zahra ta tsayar da bayanin da ta ke yi ganin wani tattausan murmushi na bayyana a kan fuskar Barrister Halima wacce ta ci gaba da tauna cingum din da ke bakinta cikin salo da gwaninta irin ta gogaggu kuma wayayyun lauyoyin da suka san aikinsu. “gaskiya kin ban mamaki Zahra, wannan dalilin ne ya sa hankalinki ya tashi duk ki ka rude kamar wata sabuwar lauya?” Jin ta yi shiru bata amsa mata tambayar da ta yi mata ba ne ya sa Halima ta ci gaba da cewa, “to in kin manta bari na tunatar da ke: ke ce dinnan dai Barrister Fatima Zahra Muhammad, ‘yadaya a wajen Marigayi I.G Muhammad Amin da matarsaJustice Aisha Sagir, kin shafe shekarudai-dai har bakwai kina aikin lauya, kin fuskanci shari’o’i masu hatsari da wuya, kin goga da manya manyan lauyoyin Senior Advocate of Nigeria da akafi sani da SANamman ba wanda ya ta6a nasara a kanki” 4(ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA DAYA, NA NURA S GARO) Barrister Halima ta yi shiru tare da dafa kafadar Zahra har a lokacin da murmushi ke karabayyane a kan fuskarta ta ci gaba da cewa, “meye abun tsoratarwa a shari’ar kisa? Ba yau kika fara fuskantar irin wannan shari’ar ba kina yin nasara a kanta illah abu daya da na sani shi ne bakya kar6ar shari’ar mutum mara gaskiya. Meye bayani akan kisan da aka yi?” Jikin Barrister Zahra a sanyaye alamun kirarin da Barrister Halima ta yi mata bai ratsata ba ta fara yi mata bayani kamar yadda saurayin ya sanar da ita. “Umar Mukhtar sunanshi budurwar tashi kuma Suhailat Adnan sun fara soyayya wata biyar da suka gabatabai saniba ashe Mahaifin yarinyar abokin gabar Mahaifinsa ne, lokacin da aka fara shirye shiryen aurensu sai Mahaifin Suhailat ya gane ko shi dan waye ya ci mishi mutunci ya tozartashi a karshe ya sa Suhailat ta daina kulashi. Ganin irin damuwar daUmar ya shiga na rashin kulashi da Suhailatta ke ne yasa Mahaifinsa ya bi bayanta har cikin gidansu a gaban Mahaifinta da Mahaifiyarta ya sanar da ita cewar ko ta amince da aurendansa ko kuma shi ne ajalinta. kwanahudu da yin hakan Suhailat tana tafiya a cikin mota Mahaifin Umar yana biye da ita a baya ya daki motarta da karfi motar Suhailat ta fada cikin kwalbatin kwatar da ke gefen titi glass ya zubo mata a jiki, kanta ya daki sitiyarin motar inda bayan wasu mintuna da kaita asibiti rai ya yi halinsa. Kin ji yadda abun ya faru Barrister” Halima ta girgiza kai babu alamun karayako fargaba a kan fuskarta ta fara lissafi da yatsunta tana nunawa Barrister Zahra. “kinga mun samu intension da action a lokaci daya, amman wannan bai isheki hujjar da za tasa ki fita da ga cikin hayyacinkiba Barrister, karki manta da cewa komai yana iya kasancewa duk da Mahaifin Umar ya yi furuci kuma ya aikata hakan bai ishi hujjar da za ta sa a ce yana sane ya kashe Suhailat ba. Zamu iya amfani da kwarewa da gogewarmu mu gano gaskiya, daga karshe kiga munyi nasara. Amman abun tambayar yanzu ta ina zamu fara?” “ban gane ba?” Barrister Zahra ta ce mata da alamun rashin fuskantar abunda Barrister Halima ke nufi. “ina nufin yana da kyau mu zauna da shi UmarMukhtardin domin ya yi mana cikakken bayani akan alakar Mahaifinsa da Alhaji Adnan” 5(ZAHIRIN KAUNA LITTAFI NA DAYA, NA NURA S GARO) Barrister Zahra ta girgiza mata kai yayin da damuwa ke kara bayyana a kan fuskarta ta kalli Halima ta ce, “duk bayaninnan da na ke miki ban san waye Umar Mukhtar ba, ta waya mukai magana da shi, na yi saurin amince mishi ne ganin yanayin halin da ya ke ciki yana neman taimako domin kuka ya ke sosai kamar wani karamin yaro. Ya cemun karna damu da sanin ko shi wane ne zan sanshi amman sai nan gaba sannan ya kirani da lambar wayarkasar Romania a karshe ya kar6i lambar Accountdina ya turamun Naira Milliyan talatin. Abun mamakin shi ne kudin da ya yi mun transfer duk da foreignaccount ne kuma da na tambayeshi ya ce mun yana Nigeria amman ya bani hakuri akan bazan samu damar ganinshi ba” Barrister Zahra ta yi ajiyar zuciya ganin yadda Halima ta kara nutsuwa tana sauraronta domin jin irin zunzurutun makudan kudin da Umar ya bayar domin a ceci rayuwar Mahaifinsa. Zahra ta ci gaba da cewa, “bawai kudin da Umar ya bayar ba ne suka sa zan shiga wannan shari’ar ba, haka kawai nakeji a jikina cewar akwai kamshin gaskiya tattare da shi da Mahaifinsa duk da ya 6oye mun hakikanin ko shi wane ne” Barrister Halima ta yi murmushi tare da tauna cingum din da ke bakinta cikin gwaninta ta ce, “aitunda har ya bada wadannan makudan kudadan ya fanshi kansa ba sai mun san ko shi wane ne ba.yanzu aiki ya rage ya namu dole mu mike tsaye domin ku6utar da Mahaifinsa indai har muka tabbatar da gaskiyarsa. Amman abun tambaya a nan shi ne wane ne Barristan da zamu kara domin musan ta hanyar da zamu biyo mishi?” “Barrister Haidar M Aliyu (SAN)…” Zahra ta bata amsa cikin sarkakkiyar murya yayinda alamun damuwar da kekan fuskarta kekara munana. “Master of law…” Barrister Halima ta kirashi da lakabun da mafiya yawan alkalai, Barristers da lauyoyi ke kiransa da shi saboda kwarewa da iya aikinsa ta fuskar shari’a. lokaci daya murmushin da ke kan fuskarta ya yaye ta daina tauna cingum din da ke bakinta domin yadda ta ji hakoranta sunyi mata nauyi ga wani dandanon daci da ta ji cingum din ya fara yi mata a baki wanda ta yi saurin sa hannu ta cireshi ta ajje a kan karamun tabledin da ke ajje a gefensu, bata mayar da kallonta kan Zahra ba sai da ta tabbatar da ta cire faringlassdin da ke makale a kan fuskarta domin wani nauyi da ta ji ya fara ga dishi dishin da ta ke gani wanda ta alakanta dukkan hakan akan faringlassdin wanda aikinsa ya karawa mutum karfin gani.

Friday, September 2, 2016

(WACECE KHADIJAH LITTAFI NA DAYA NA NURA ISA S GARO)
1 Dakin asibitin ya yi shiru, ba ka jin motsin kowa sai kukan mace guda daya da ta sa mara lafiyan a gaba. yar dattijuwar matar dake gefen ta ita ma idanuwanta sun ciko da kwalla ta kalli likitan dake ta faman aikin gwaje, gwaje a kan mara lafiyan.
Ta ce,
Yanzu Doctor Ahmad kana nufin idan Nura yakai gobe be farka ba ze mutu?.
Doctor Ahmad ya danyi shiru kamar ba ya san Magana, sannan.
Ya ce,
Hakane hajiya, bana zatan in ya kuma awa ashirin da hudu be farka ba, ze kuma wani numfashi a duniya
Ya ba ta amsa a lokacin da ya ke kokarin gyara kwanciyar mara lafiyan.
Dattijiwar matar ta goge hawayan da ke ta fita da ga idanta sannan
Ta ce,
Bazan iya jure ganin Nura a cikin wannan hali ba Doctor, dan haka, ina san ka bincika min asibitin da zanje cikin fadin duniyar nan, kafin wadannan awanni su cika
Likitan ya kalleta ya ce,
Hajiya bana zatan duk asibitocin duniyar nan in zasu taru akan Nura akwai wani taimakwan da za su iya yi mai, domin kuwa abin dake faruwa a kanshi bakwan abune a duniyar ilimin likitanci ta duniya. a iya bincike na, lafiayarsa kalau ba abin dake damunshi, illa rashin kwarin jiki saboda tsawon lokacin daya dauka beci abinci ba,
Wasu tagwayan hawaye suka fito da ga idanuwanshi yai saurin sa gefen rigarsa ya goge, sannan ya ci gaba da cewa.
Dafarko na zaci barci ya ke, amman tsayin kwanakin da ya shafe be farka ba ne suka tabbatarmin ba lafiyarsa kalauba, nayi kokari na turawa babban sashin asibitin mu dake kasar England irin abinda na ke fuskanta akan mara lafiyan. bayan sun bincika suka tabbatar min da basu sami wata mafita ba game da wannan matsalar. Bayan haka suka sanar dani cewar tsayin kwanakin da ya dauka be ci komai ba in har ya kara awa ashirin da hudu be farka ba mutuwa ze yi, domin yanzu ha ka lakar jikinshi ta yi rauni sosai
Likitan ya na zuwa nan a zancensa dattijuwar ta fashe da kuka. yarinyar da ke gefen mara lafiyan kuma ta sa hannu ta na jijjiga mara lafiyan da karfi cikin kuka ta na ce wa.
Dan Allah Noor ka tashi, in ka mutu nima bazan iya rayuwa ba.
Da sauri Doctor Ahmad ya ture hannuwan yarinyar daga jikin mara lafiyan. sannan cikin fushi ya fara yi mata Magana.
Jijjigashin da ki ke ba ze sa ya mutu ba har sai kwanan shi ya kare. kar kiji an ce ba ze kara awa ashirin da hudu ba kiyi farin ciki. idan Allah ya yi akwai kwanan shi a gaba dole ya farka.
Yai shiru. wasu hawaye da yai kokarin 6oyesu suka samu damar sauka akan fuskar sa. muryarshi na rawa alamun kukan da ya ke ya fara cin karfinsa ya ci ga ba da ce wa.
Sau uku kina dukanshi ya na suma. kin ji mai manya-manyan raunuka sunfi a kirga. Amman bawan Allah nan be ta6a nuna miki damuwarsaba illa ma kokarin ganin ya kwantar miki da hankali da ya ke. Ke kuma hakan be sa kin janye aniyarki ta kokarin kashe shin da kike ba
Kuka ne yaci karfin Doctor Ahmad yai shiru ya fara kokarin saita numfashinsa da ke kokarin daukewa. Daya daga cikin nurses din da ke dakince ta ce,
Kayi hakuri ha ka Doctor ka san kana da ciwan zuciya, in ka sawa kanka damuwa ako da yau she jininka ze iya hawa.
Ba tare da ya kalle ta ba ya ce,
Ba komai Maryam nagode da kulawar da kike ba ni
Sannan ya waiga gun dattijuwar da har a lokacin bata daina kukan da take ba. ya na kokarin yi mata magana ne hannun mara lafiyan ya fara motsi. cikin sauri ya maida hankalinsa gun mara lafiyan domin kwana tara kenan da kawo mara lafiyan amman ko yatsansa be ta6a motsawaba duk da kokarin da likitan yai tayi na ganin ya farkar da shi, amman ya kasa cin nasara saboda yanayin da mara lafiyan ya nuna kamar ya mutu alhalin kuma ya na numfashi, illah rashin motsi da ga6o6insa ke yi, sai yanzu da idanunsa suka gane mai motsin da maralafiyan ya yi.