(WACECE KHADIJAH LITTAFI NA DAYA NA NURA ISA S GARO)
1
Dakin asibitin ya yi shiru, ba ka jin motsin kowa sai kukan mace guda
daya da ta sa mara lafiyan a gaba. yar dattijuwar matar dake gefen ta
ita ma idanuwanta sun ciko da kwalla ta kalli likitan dake ta faman
aikin gwaje, gwaje a kan mara lafiyan.
Ta ce,
Yanzu Doctor Ahmad kana nufin idan Nura yakai gobe be farka ba ze mutu?.
Doctor Ahmad ya danyi shiru kamar ba ya san Magana, sannan.
Ya ce,
Hakane hajiya, bana zatan in ya kuma awa ashirin da hudu be farka ba, ze kuma wani numfashi a duniya
Ya ba ta amsa a lokacin da ya ke kokarin gyara kwanciyar mara lafiyan.
Dattijiwar matar ta goge hawayan da ke ta fita da ga idanta sannan
Ta ce,
Bazan iya jure ganin Nura a cikin wannan hali ba Doctor, dan
haka, ina san ka bincika min asibitin da zanje cikin fadin duniyar nan,
kafin wadannan awanni su cika
Likitan ya kalleta ya ce,
Hajiya bana zatan duk asibitocin duniyar nan in zasu taru akan
Nura akwai wani taimakwan da za su iya yi mai, domin kuwa abin dake
faruwa a kanshi bakwan abune a duniyar ilimin likitanci ta duniya. a iya
bincike na, lafiayarsa kalau ba abin dake damunshi, illa rashin kwarin
jiki saboda tsawon lokacin daya dauka beci abinci ba,
Wasu tagwayan hawaye suka fito da ga idanuwanshi yai saurin sa gefen rigarsa ya goge, sannan ya ci gaba da cewa.
Dafarko na zaci barci ya ke, amman tsayin kwanakin da ya shafe be
farka ba ne suka tabbatarmin ba lafiyarsa kalauba, nayi kokari na turawa
babban sashin asibitin mu dake kasar England irin abinda na ke fuskanta
akan mara lafiyan. bayan sun bincika suka tabbatar min da basu sami
wata mafita ba game da wannan matsalar. Bayan haka suka sanar dani cewar
tsayin kwanakin da ya dauka be ci komai ba in har ya kara awa ashirin
da hudu be farka ba mutuwa ze yi, domin yanzu ha ka lakar jikinshi ta yi
rauni sosai
Likitan ya na zuwa nan a zancensa dattijuwar ta
fashe da kuka. yarinyar da ke gefen mara lafiyan kuma ta sa hannu ta na
jijjiga mara lafiyan da karfi cikin kuka ta na ce wa.
Dan Allah Noor ka tashi, in ka mutu nima bazan iya rayuwa ba.
Da sauri Doctor Ahmad ya ture hannuwan yarinyar daga jikin mara lafiyan. sannan cikin fushi ya fara yi mata Magana.
Jijjigashin da ki ke ba ze sa ya mutu ba har sai kwanan
shi ya kare. kar kiji an ce ba ze kara awa ashirin da hudu ba kiyi farin
ciki. idan Allah ya yi akwai kwanan shi a gaba dole ya farka.
Yai shiru. wasu hawaye da yai kokarin 6oyesu suka samu damar sauka
akan fuskar sa. muryarshi na rawa alamun kukan da ya ke ya fara cin
karfinsa ya ci ga ba da ce wa.
Sau uku kina dukanshi ya
na suma. kin ji mai manya-manyan raunuka sunfi a kirga. Amman bawan
Allah nan be ta6a nuna miki damuwarsaba illa ma kokarin ganin ya kwantar
miki da hankali da ya ke. Ke kuma hakan be sa kin janye aniyarki ta
kokarin kashe shin da kike ba
Kuka ne yaci karfin Doctor
Ahmad yai shiru ya fara kokarin saita numfashinsa da ke kokarin daukewa.
Daya daga cikin nurses din da ke dakince ta ce,
Kayi hakuri ha ka Doctor ka san kana da ciwan zuciya, in ka sawa kanka damuwa ako da yau she jininka ze iya hawa.
Ba tare da ya kalle ta ba ya ce,
Ba komai Maryam nagode da kulawar da kike ba ni
Sannan ya waiga gun dattijuwar da har a lokacin bata daina kukan
da take ba. ya na kokarin yi mata magana ne hannun mara lafiyan ya fara
motsi. cikin sauri ya maida hankalinsa gun mara lafiyan domin kwana tara
kenan da kawo mara lafiyan amman ko yatsansa be ta6a motsawaba duk da
kokarin da likitan yai tayi na ganin ya farkar da shi, amman ya kasa cin
nasara saboda yanayin da mara lafiyan ya nuna kamar ya mutu alhalin
kuma ya na numfashi, illah rashin motsi da ga6o6insa ke yi, sai yanzu da
idanunsa suka gane mai motsin da maralafiyan ya yi.